An ƙera motar yaƙi a Uganda


Shugaban rundunonin ƙasa na Uganda, janar Muhoozi Kainerugaba ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na wasu motocin yaƙi da ya ce an ƙera a ƙasar.

Ya ce an tsara kuma an ƙera motocin a Uganda amma bai bayyana abubuwan da ta ƙunsa ba da farashinta.

Sunan motar Chui, wanda ke nufin Damisa a harshen Swahili kuma Shugaba Yoweri Museveni ne ya ƙaddamar da motar.

BBC Hausa

Previous Post Next Post