Gwamnan arewa ya lashi takobin kawo Karshen bangar siyasa a jiharsa


Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi gargaÉ—in cewa duk wani É—an siyasa da aka kama da É—aukar nauyin Æ´an bangar siyasa a jihar zai fuskanci hukunci yadda ya dace da shi, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta É—auki rashin É—a'a ba.

Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Litinin a gidan gwamnati a lokacin da yake jawabi a gaban shugabannin wata ƙungiya ta ƴan bangar siyasa.

Wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafofin yada labarai, Isa Gusau, ya fitar ta ce gwamna Zulum ya sha bayar da umarnin ayyuka da shirye-shiryen koya wa al'umma hanyoyin dogaro da kai ga ƙungiyoyin don mayar da su halatattu.

Jihar ta ce duk da waÉ—annan matakan, gwamnan ya koka kan yadda mafi yawan matasa a jihar suka É—auki bangar siyasa a matsayin sana'a.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN