Da Duminsa: Rikici ya kunno kai a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan zabe


Rikicin da ya barke a cikin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya dauki wani sabon salo na daban.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa bangaren da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, ya kaddamar da babban jami’in gudanarwar sa.

A cewar rahoton, an yi bikin ne a Freedom House, sakatariyar yakin neman zaben da Sanata Abe ya kafa a GRA ta Fatakwal.

Jami'an sun hada da Golden Chioma a matsayin shugaban jam'iyya na jihar, Mike Amakiri, Mataimakin Shugaba, Inye Jack a matsayin Sakatare, da Joy Woko, shugabar matan jam'iyya a jihar.

Yayin da yake zantawa da manema labarai Chioma ya ce akwai majalisun unguwa, na kananan hukumomi da na jihohi da aka samar daga bangaren, sannan ya yi kira ga gwamna Nyesom Wike da ya shirya mika mukamin.

A halin da ake ciki, Emeka Beke dan tsagin ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya zama shugaban jam'iyyar bayan ya samu kuri'u 1,570 inda ya kayar da Chizy Nyemosele, in ji jaridar The Nation.

Mathew Adoyi-Omale, sakataren kwamitin majalisar gangamin ta jihar Ribas wanda ya sanar da sakamakon, ya bayyana tsarin zaben a matsayin na gaskiya da adalci.

Sai dai, Chioma, wanda ya fice daga takarar kujerar shugabancin a karshe ya bayyana tsari da sakamakon zaben a matsayin mara inganci.

Ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN