Allah Sarki: Duba matar da ta 'san' ranar da za ta mutu


Martha Sepúlveda ta yi farin ciki domin za ta kawo ƙarshen rayuwar ta a ranar Lahadi, 10 ga Oktoba, da ƙarfe 7 na safe.

Ta yi murmushi a gaban masu ɗaukar hoto, tana cin wani abinci mai suna guacamole kuma tana shan giya a wani gidan abinci a Medellín, Colombia, duk da tana gab da mutuwa.

Tana farin ciki ba don komai ba sai don kotu ta ba da izinin a yi mata 'euthanasia', wato allurar mutuwa.

A Colombia, an halatta yin euthanasia a 1997, amma sai a 2015 ta zama doka. Tun daga wannan lokacin, an yi wa mutane 157 allurar.

Amma a watan Yulin da ya gabata, kotun ƙasar ta faɗaɗa ƴancin yin allurar ga wadanda ke cikin "matsananciyar wahala ta jiki ko ta hankali" dalilin wata cuta da ba a warkewa.

Kuma a kan Martha Sepúlveda aka fara ba da damar yin euthanasia ga mara lafiyar da ke fama da cutar da ba ta ajali ba.

Tun lokacin da aka gano tana da cutar da ta shafi jijiyoyi (myotrophic lateral sclerosis ALS) kuma cuta mai tsanani da ba a iya warkewa, rayuwarta ta kasance cikin azaba.

Ta yi imanin cewa mutuwarta za ta yi jinkiri da tsananin wahala. Sai wata rana ta gaya wa Federico, ɗanta ɗaya tilo mai shekaru 22, cewa tana son ta yi fafutuka a yi mata euthanasia. Ta ko samu.

Abin ban mamaki, samun damar mutuwa ya dawo mata da farin cikin rayuwarta.

"Mahaifiyata tana cikin natsuwa da farin ciki saboda sun ce za ta iya mutuwa saboda rayuwarta a zahiri mai cike da azaba ce," kamar yadda ɗanta ya shaida wa BBC.

Kuma haka take, tana farin cikin cewa za ta mutu.

"Ina da sa'a," in ji ta a hirarta ta ƙarshe da gidan talabijin na Caracol. "Ina yawan yin dariya, ina bacci cikin nutsuwa."

"Ni ƴar Katolika ce, ina ɗaukar kaina a matsayin mai imani ƙwarai. Amma Allah ba ya son ya ga ina shan wahala. Yadda nake fama da wannan cutar ta lateral sclerosis, mafi kyawun abin da zai iya faruwa da ni shi ne in mutu in huta . "

A nan ƙasa, karanta bayanin ɗanta, Federico Redondo Sepúlveda, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Mahaifiyata ta kamu da cutar amyotrophic lateral sclerosis a ƙarshen 2018.

Ta amshi bayanin likita ta wata hanya da ita ce kawai ta fi ganewa- dariya ta yi. Ta ce "duba, ina da wannan cutar kuma zan mutu cikin shekaru uku." Amma ta yi magana cikin raha sosai, tana barkwanci.

Mahaifiyata ta kasance marar tsoron mutuwa. Kullum ta kan ce: "Ba na tsoron barin duniya, sai yadda zan tafi", wanda shi ne dalilin da ya sa ta nemi a ba ta haƙƙinta na yin mutuwa mai daraja.

An gano Martha na da cutar amyotrophic lateral sclerosis a ƙarshen 2018

Ba ta amince da ƙare rayuwarta kwance a kan gado ba. Idan ciwon amyotrophic lateral sclerosis ya zo ƙarshe, mai fama da shi ba ya iya magana, ba ya iya hadiye abinci... cuta ce mai matuƙar raɗaɗi kuma ga mahaifiyata cuta ce marar martaba.

An gano tana da cutar ne cikin ƙanƙanin lokaci. Daga baya, sai ta fara rasa ƙarfi a ƙafafunta, tana buƙatar taimako don yin tafiya mai tsawo ko gajeriyar tazara. Daga baya, sai ta fara buƙatar taimako kan ko wace irin tafiya, har a cikin gida.

Kuma a farkon wannan shekarar ta fara buƙatar taimakon don shiga banɗaki. Sannan dole ne a yi mata wanka, a sanya mata sutura. Wani lokacin cin abinci ko goge baki na da wahala a gareta saboda hannayenta suna rasa ƙarfinsu.

Babban abin da ya fi muni a gareta shi ne ganin yadda ta sauya har ta kai ga ba za ta iya yi wa kanta abubuwa na yau da kullum ba.

Martha tare da ɗanta Federico

Wata rana ta ce da ni, "Zai yi kyau idan zan iya neman euthanasia." Kuma, ban ɗauki abin da ta ce da mahimmanci ba.

Amma da ta gaya min tana son yin haka, sai na ki amincewa na wasu kwanaki. Na ce, "a'a, mahaifiyata, ba yanzu ba." Na ce, "Mama, don Allah kar a yi."

Ina kallon kaina a matsayin mutum mai sassaucin ra'ayi, na yi tunanin haƙƙin euthanasia dama ce da yakamata a kiyaye, amma ban taɓa tunaninta a nan kusa ba.

Daga baya, na yi la'akari da mawuyacin halin da take ciki, da yanke ƙauna da rashin mutuncin da ta tsinci kanta a ciki, ta ce, "Ina ganin zan iya ƙara nuna soyayyata gareta idan na tallafa mata a wannan shawarar da ta yanke."

Ina buƙatar mahaifiyata kuma ina son ta kasance tare da ni a ko wane hali. Amma a wannan yanayin, zan kasance ina tunanin kaina ne kawai, game da buƙatuna.

Mun yi shekaru 22 tare. Rayuwata ta ta'allaƙa a kanta, kuma ita ma haka. Bayan tafiyarta, dole ne in ƙirƙiri wata rayuwar. Shi ya sa daga farko abin ke da wahala kenan.

Lokacin da na kula da ita, na kasance cikin yau farin ciki gobe baƙin ciki. A gefe guda ina son matakin, saboda ina ganin cewa ko ta yaya ina saka wa mahaifiyata ne, duk goyon baya da duk abin da ta yi min a duk tsawon rayuwata.

Amma ina kuma tunanin abin da take gaya min. Ta ce da ni, "Ɗana, wannan ba rayuwa ba ce, wannan ba ta da daraja."

Babu shakka ina cikin baƙin ciki. Ina cikin damuwa, a fili Ina ... matsananciyar wahala ta wata hanya. Zai zama abin mamaki idan ba haka ba.

Martha Sepúlveda a wani tsohon hoto tun tana da ƙuruciya

Amma kuma ina ɗan samun sanyi a raina ta yadda mahaifiyata ta iya kawo ƙarshen rayuwarta yadda take so. Ranar da lokacin da take so.

Tun tana ƙarama ta ce ba ta taɓa so ta yi ciwon da zai sa ta kasance a kwance a kan gado ba, ta kasance ta dogara da wani a ko yaushe.

Mun yarda cewa sai da rayuwa ake iya yanke shawara, kuma tun da cutar ta fara yi wa mahaifiyata rauni a zahiri, ba ta iya yanke wa kanta hukunci ko shawara.

Mutane da yawa suna mamaki domin suna ganinta cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

Mahaifiyata tana cikin nutsuwa da farin ciki saboda likitoci sun gaya mata cewa tana iya mutuwa saboda rayuwarta a zahiri mai wahala ce. Ba haka take a da ba.

A baya ina cikin matsananciyar damuwa, baƙin ciki da yanke ƙauna da rayuwa.

Amma yanzu mahaifiyata za ta mutu ranar Lahadi da karfe bakwai na safe. Kuma tana farin ciki saboda ta san cewa za a yi amfani da tsarin euthanasia.

A ranar Lahadiaka binne ta - aka ƙona gawarta, za a yi bikin binne ta kuma shi ke nan, saboda ainihin abin da ta ke so kenan.

Zan yi kewar ta sosai. Na yi imani babu abin da ba zan yi kewa ba a game da ita, domin komai zai sauya.

Daga murmushinki zuwa karsashinki da kyawawan halayenki kan abubuwa masu kyau da marasa kyau a rayuwa ... zuwa tsawatarwarki.

Zan yi kewar komai.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN