Yadda yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa


Ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust.

Ƴan bindigan sun janye kai hare-hare a garuruwa tun bayan da gwamnatin jihar ta soke cin kasuwannin mako-mako don daƙile rashin tsaro.

Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

Yunwa ya fitini 'yan bindigan Kaduna, sun fara tambayar girki a matsayin kudin fansa. Hoto: Daily Trust

Wani shugaban matasa a ɗaya daga cikin ƙauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro ya shaidawa Daily Trust cewa tun bayan hana cin kasuwanni ƴan bindiga da ke sace mutane a ƙauyukan Kutemashi da Kuyello dafaffen abinci suke tambaya duk lokacin da suka sace mutane.

A cewarsa, hana siyar da man fetur a gidajen mai da ke ƙauyuka ya taimaka wurin rage zirga-zirgan mutane.

Ya ce:

"An fara samun zaman lafiya a Dumari, Kuyello, Kutemashi, ƴan bindiga sun dena kai hari. A daji suke tsayawa suna kwace abinci galibi dafaffen abinci daga masu sayarwa."

Ya kara da cewa idan sun sace mutum uku, suna ƙyalle guda ɗaya ya tafi guda ya kawo musu abinci daga wurin ƴan uwansa tunda babu hanyar sadarwa.

Shugaban matasan ya kara da cewa har yanzu ba a samu cikakken tsaro ba a Dogon Dawa domin mutane suna tsoron zuwa gonakin su.

Babangida ya ƙara da cewa hana hawa babura wadanda ba na haya ba ya jefa mutanen gari da ƴan bindigan a cikin mawuyacin hali.

Daya daga cikin wanda abin ya faru da su wacce ta ce sunanta Iklima Murtala, ta yi ikirarin cewa mutane 17 sun mutu saboda tsananin yunwa, ruwaiyar Daily Trust.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Zamfara, Ayuba Elkana, ya ce saboda matsin lambar da rashin abinci, 'yan bindigan sun tsinci kansu a mawuyacin hali.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN