Yanzu yanzu: An yi yunkurin juyin mulki a kasar Sudan, sojin Gwamnati sun dakile yunkurin sun kama wasu masu juyin mulki


An gudanar da juyin mulki da bai yi nassara ba da sanyin safiyar Talata a kasar Sudan da bai yi nassara ba. Gidan Talabijin na kasar ya labarta.

Shafin isyaku.com ya samo cewa Kakakin hukumar sojin Sudan Mohamed al-Faki Suleiman, ya ce soji madu biyayya ga shugaban kasa da kasar Sudan, sun dakile yunkurin juyin mulkin.

Ya ce an kama wasu daga cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin kuma za a fara yi masu tambayoyi ba da dadewa ba.

Ya ce an shawo kan lamarin kuma al'amurra sun ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Previous Post Next Post