NSCDC jihar Kogi ta ce jami'inta da aka kama tare da masu satar mutane korarre ne daga rundunar


Rundunar tsaron farin kaya NSCDC ta jihar Kogi ta ce Abdullahi Saidu da aka kama tare da masu satar mutane don karbar kudin fansa ba jami'inta bane domin ya tsere daga wajen aiki mako biyu kafin a kama shi tare da masu satar mutane. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Yan Banga a jihar Kogi ne suka kama Saidu bisa zargin rawa da yake takawa na ba masu satar mutane bayanan sirri domin karbar kudin fansa tare da ba su makaminsa na aiki domin su gudanar da satar mutane su raba kudin.

Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Kogi Suleiman Mafars ya sanar wa manema labarai ranar Litinin 20 ga watan Satumba. Ya ce Saidu ya riga ya tsere daga bakin aikin hukumar sati biyu kafin dubunda ta cika.


Previous Post Next Post