Aikin sanata ya fi karfin albashin N13m duk wata, muna bukatar kari - Rochas


Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus-alawus bai kai wahalar aikin da 'yan majalisar ta dattawa ke yi ba.

Rochas wanda shi ma dan majalisar dattawa ne ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Tsohon gwamnan na Imo wanda ke gardama kan ya kamata a rage yawan sanatoci da aka zaba daga kowace jiha zuwa uku ya ce albashin sanata ya kai kimanin naira miliyan biyu tare da alawus na gida na naira miliyan uku da sauran alawus na kusan miliyan 11.

A cewarsa:

"Amma, hakan bai isa ba saboda idan muna da sanata, ya kamata mu biya shi da kyau domin yin aikin da gaske saboda ba shi da wani aiki sai dai kuma idan muna son a yi aikin na dan lokaci ne."

Ya kamata a rage kudin gudanar da mulki

A bangare guda, ya jaddada bukatar rage kudaden gudanar da mulki a Najeriya da nufin habaka kudi ga kasar.

“Ku tuna, na fadi ya kamata a samu sanata daya a kowace jiha amma hakan ya tayar da cece-kuce a kasar baki daya.

"Amma, jim kadan bayan na yi magana game da hakan Italiya ta rage adadin sanatocinta da kashi 60 cikin dari kamar dai sun ji daga gare ni.

“Kun san Najeriya za ta so a ci gaba da bin tsohuwar hanya, amma idan kuka ci gaba da yin abubuwa kamar yadda kuka saba za ku ci gaba da samun tsohon sakamako, don haka dole ne mu gwada sabon abu.

“Yanzu, da kuke magana game da rage kudaden gudanar da mulki, Najeriya za ta fi kyau a ce tana da sanata daya a kowace jiha da kuma membobin majalisar tarayya uku a kowace jiha. Wannan adadin mutanen na iya magance matsalolin tsarin mulkin Najeriya."

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Rochas Okorocha, sanata mai wakiltar Imo ta yamma kuma tsohon gwamnan jihar ta Imo, ya ce hangen nesan sa na hada kan Najeriya yana saka shi ya ji kamar zai hauka.

Okorocha ya yi wannan magana ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da manema labarai da kungiyar 'yan jaridaN Najeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya (FCT).

FCT NUJ ta karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Imo ne gabanin shirin murnar cikarsa shekaru 59 a duniya, The Cable ta ruwaito.

Da yake amsa tambaya kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023, Sanatan ya ce:

Ba ni da burin zama shugaban kasa amma hangen nesa na samun hadin kan Najeriya na haukata ni."

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN