Ana tsoron akalla mutum 30 sun rasa rayukansu yayinda aka kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
A cewar tsohon shugaban gamayyar matasan Kaura, Derek Christopher, yan bindigan sun dira garuruwan ne misalin karfe 5 na yammacin Lahadi suka bude musu wuta, rahoton Daily Trust.
A cewarsa:
"An garzaya da wasu asibiti don jinyarsu."
Legit tayi yunkurin tuntubar Kakakin hukumar yan sanda a jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, amma bai daga wayarsa ba.
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka