Type Here to Get Search Results !

Duba jerin ababe 8 da gwamnonin arewacin Najeriya suka ce a taronsu - ISYAKU.COM


Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi wani taro na musamman a kan abubuwa da dama da suka hada da matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.

Taron na ranar Litinin ya samu halartar gwamnoni da 'yan majalisar dokoki da kuma sarakunan gargajiya, karkashin jagorancin Sarkin Musulmai na Najeriya Alhaji Sa'ad Abubakar II.

Kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya bayyana, taron na gaggawa ne don nazarin halin da lardin arewacin Najeriyar ya samu kansa musamman ta bangaren tsaro.

Hasali ma, shugaban kungiyar gwamnonin ya ce taron, wani zama ne na yin waiwaye ga kudurorin da suka zartar a wani taro makamancinsa da suka yi a watan Fabrairun wannan shekarar.

Kenan a wannan zaman za su yi kididdiga ko nazarin yadda aka aiwatar da wadansu shawarwarin da suka zartar a wancan lokacin, musamman ma abubuwan da suka shafi yankurin wanzar da zaman lafiya da ci gaban yankin, ciki har da batun inganta tsaro da kyautata tattalin arziki da walwalar al'umma.

Kazalika a wancan zaman an yi magana a kan hanyoyin da za a bi wajen tunkurar kalubalen da ya shafi masu gudun-hijira, har ma aka yi tunanin hada-gwiwa da gwamnatin tarayya da wadansu gwamnatoci da ke wasu sassan Najeriya don samun kyakkyawan sakamako.

Mista Lalong ya ce kungoiyar gwamnonin arewacin Najeriyar ta samu sakamako daga kamfanoni da daidaikun jama'a, wadanda aka bukaci su gudanar da bincike, ko kuma su aiwatar da wadansu ayyuka, yayin da kuma take dakon rahoto daga wadanda ba su kai ga gabatar da nasu ba.

Kuma a wannan zaman ne za su yi nazarin kwakwaf ga rahotannin da suka shiga hannu.

Ga dai wasu muhimman abubuwa da taron ya mayar da hankali a kai:

1. Kungiyar ta sake nazari kan batun sha'anin tsaro na baya-bayan nan daga yankin, ta kuma gano cewa akwai bukatar hada kai da kara kokari tsakanin gwamnatin Tarayya da jihohin arewacin kasar, a yayin da ta kuma yi duba kan matakan baya-bayan nan da aka dauka.

Taron ya kuma nuna damuwa kan matsalolin da jami'an tsaro ke fuskanta sannan ya nemi rundunar soji ta kaddamar da wani aiki ba kakkautawa, tare da bayar da bayanai ga sauran yankunan kan shirye-shiryensu na tunkarar matsalar.

2. Kungiyar ta yaba wa aikin da ake yi na kai hare-hare kan 'yan fashin daji da masu satar mutane da kungiyar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashi da wasu bangarori na arewa maso yammacin da arewa ta tsakiyar Najeriya.

Ta kuma karfafa wa dakarun tsaro da sauran hukumomin tsaro gwiwar ci gaba da yin hakan don a tabbatar da cewa an magance matsalar rashin tsaron baki daya cikin kankanin lokaci.

3. Kungiyar ta kuma karbi rahoto kan shirin samar da wutar lantarki na hasken rana ta kuma bayyana cewa an gabatar da batun samun filin da za a kaddamar da shirin kuma jihohin arewacin kasar na duba lamarin.

4. Taron ya kuma karbi bayanai kan ayyukan wasu kwamitoci da kungiyar gwamnonin arewa ta kaddamar tare da cewa an amince da shawarwarin da aka bayar inda za a gabatar da matakan da za a bi.

5. Kungiyar ta ce wasu gwamnonin arewacin Najeriya tun da fari sun bayyana ra'ayinsu na bin tsarin karba-karba zuwa ga shiyyoyi uku na kudancin kasar da nufin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a kasar.

Sai dai kuma kungiyar ta yi Allah-wadai da matsayar takwarorinsu na kudu cewa dole a mika shugabancin kasar ga yankin kudanci.

6. Kungiyar gwamnonin arewacin ta kuma duba batun karbar harajin VAT da ake ta yi a kasar.

"A matsayinmu na shugabannin da suka san ya kamata, duk da cewa mun san cewa batun na gaban, amma don sanar da mutane halin da ake ciki za mu bayyana wasu abubuwa kamar haka:

7. Sarakunan gargajiya sun yaba da kokarin da kungiyar gwamnonin arewa ke yi zuwa yanzu wajen warwware muhimman matsalolin da jihohin arewacin Najeriya ke fuskanta.

8. Kungiyar ta koka kan girman tuggun da wasu jami'an bangaren shari'a ke kitsawa ta wajen sakin miyagu daga gidan kaso da ba da belinsu.

"Wannan halayya na kawo cikas wajen yakin da ake yi da miyagun laifuka, don haka akwai bukatar inganta tattara bayanan sirri tsakanin jihohin."

BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies