Duba hukuncin ɗauri da Kotu ta yi ga matashin da ya kashe ƙanwarsa da duka saboda ta tara samari 6


Alkalin babbar kotun Bulawayo, da ke Zimbabwe, Justice Maxwell Takuva ya yanke wa wani saurayi mai shekaru 27 dan asalin Gweru a Zimbabwe shekaru 8 a gidan gyaran hali bayan ya yi wa kanwarsa mai shekaru 16 duka wanda ya yi sanadin mutuwar ta bisa zargin ta da rashin kamun kai.

Saurayin, Terrence Tarisai na Clifton Park ya musanta zargin da ake masa na halaka kanwar sa Tryphine, ya dake ta wanda har ta kai ga mutuwa bayan ya bincike sakonnin wayar ta na kafar sada zumuntar WhatsApp inda ya gano yarinyar ta tara samari har 6.

Ya dake ta ne bayan ya dawo gida bai tarar da ita ba

Kamar yadda LIB ta ruwaito, an samu rahotanni akan yadda Tarisai ya dawo gida ranar 22 ga watan Yulin 2020 bai ga Tryphine ba inda ta bar kanwar ta mai shekaru 10 ita kadai a gida.

Tryphine wacce ‘yar aji 3 ce a Ascot High School dake Gweru ta dawo gida karfe 6 na yamma. Ta bayyana wa yayan ta cewa a shago ta tsaya.

Saidai Tarisai bai yarda da bayanin ta ba ya kwace wayar ta ya bincike sakonnin ta na WhatsApp inda ya gane ta na tara samari da yawa. Daga nan ya zarge ta da rashin kamun kai.

Ganin hakan ne ya sa Tryphine ta gudu gidan antin ta dake Mtapa yanki na 7 a Gweru. Washegari da safe antin Tryphine ta raka ta gida.

Sai da ya yi mata duka kashi biyu

Duk da antin ta yi masa magana kuma ta bashi hakuri sai da ya samu wata bulala ya yi mata dukan tsiya kuma ya bukaci ta dakatar da alakar ta da duk samarin ta. Daga nan ya ci gaba da dukan ta.

Bayan ta sha duka kamar bakuwar karya, sai Tryphine ta fara korafin tana jin sanyi don hakan antin ta ta daura ta a gado don ta huta. Daga nan ne ta rasu bayan ta kwashe sa’o’i tana bacci. Bayan an gano ta rasu ne ‘yan sanda su ka kama Tarisai.

Alkalin kotun da ya yi hukunci ya ja kunnen jama’a akan amfani da karfi wurin tankwasa yara. Kamar yadda LIB ta ruwaito, Justice Takuva ya ce:

“Akwai bukatar iyaye da magabata su dena amfani da karfi mai yawa wurin tankwasa yara saboda hakan ya ja an rasa rayuka da dama. Ga shi yanzu an rasa ran yarinya karama. Sakamakon dukan cutarwa da ya yi mata an yanke ma sa hukuncin shekaru 8 a gidan gyaran hali."

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN