Yan bindiga sun sace dan uwan wani SSG Sakataren gwamnatin jihar arewa


Yan bindiga sun sace Alhaji Kabir Muhammed, dan uwan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha Muhammed a Kano.

Kabir na gudanar da wani aiki ne a gonarsa a kauyen Daftau da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Kano kafin Yan bindigan su sace shi a gonar ranar Laraba 1 ga watan Satumba.

Makwabta sun kula cewa dattijon mai shekara 80 bai je Sallar Subahi ba, sakamakon haka aka gano abin da ya faru da shi.

Previous Post Next Post