Zamantakewa: Me ya sa tarbiyyar samari ta yi faduwar bakar tasa?


Teburin da na jijjiga na tabo batun lalacewar tarbiyyar 'yan mata a satin da ya wuce dai na san lamarin ba sauki. To 'yan mata kar ku kaga min adawa, yau dai ga ni zan girgiza teburin samari 'yan bana-bakwai.

Yadda duk ake son mace ta-gari don gina gida da iyali, to tabbas haka ake son namiji na-gari don samun uban kirki.

Ban taba yarda da batun wasu masu cewa iskancin namiji ado ne ba. Lalacewa duk sunanta lalacewa.

Abin bakin ciki ne a ce yawanci samari a zamanin nan ba sa ganin kan kowa da gashi.

To yau don lalacewa an zo zamanin da yaro zai je social media ya kalli sa'ar babarsa ko babansa ya dankara musu zagi ba kunya ba tsoron Allah.

Sannan ga wata halayya ta wasu samarin masu sakin wando can kasa-kasan kugunsu, suna tafiya yana zamewa.

Ga bala'in shaye-shayen miyagun kwayoyi da ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a zamanin nan. Wasu samarin kuma ga 'yar banzar karya da yaudara da son lalata 'ya'yan jama'a.

Wasu kuma ba a yi musu tarbiyyar girmama na gaba da su ba ne balle sanin darajar matar da suka aura.

Sun mayar da mace abar banza, duka da zagi da cin mutunci ya zama sana'arsu. Da an yi aure kwana biyu an yi saki. Lamarin dai sai addu'a kurum.

Sannan akwai wata al'ada ta gallabar mazauna unguwanni da tseren motoci marar dalili, lamarin da ke sa a dinga samun munanan hadurra har da rasa rayuwa.

A wasu yankunan kuma kilisar dawakai da samarin suka bullo da ita ita ce take dagawa al'umma hankali. A dinga sukuwa da dawakai ba tsari, wanda hakan ke sa shi ma ake yawan samun hadurra.

Ga shi ba sa ganin kan kowa da gashi balle a yi magana su ji.

Ta yaya za mu gyara ne?

Sheikh Nuru Khaild ya ce matakan gyaran tarbiyyar samari a zamanin nan sun hada da:

  • Janyo su a jiki da nuna musu cewa suna da muhimmanci
  • A dinga jin ta bakinsu kan abin da suka fahimta dangane da halin rayuwa.
  • A dinga ba su damar gwada basirar da Allah Ya ba su
  • Kar a dinga kushe tunaninsu, amma a dinga gyara musu kura-kuransu
  • A dinga ba su shawarwari.
Wannan layi ne

Wasu na baya da za ku so ku karanta


Karin wasu abubuwan sun hada da; kar a bata yaro da nuna masa gatan dukiya da arziki sannan a saka masa ido ba a kwabarsa.

Wata fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa Anty Bilkin Funtuwa ta taba ce min, ya kamata kowace mace ta raini danta ya taso tamkar dan sarauniya.

Ta ce abin da take nufi da dan sarauniya shi ne wanda za a yi masa tarbiyyar da zai tsaya da kafafunsa, ya iya neman na kansa, ya dinga ganin girma da darajar mutane.

Shi ne wanda idan ya auri mace zai dinga tausayi da jin kanta da kyautata mata. Ya zamto wanda duk wata kwaramniya ba za a ganshi a ciki ba.

Ana iya yi wa namiji tarbiyya ta yadda zai kula da gida da iyali da sauke hakkoki tun yana yaro kamar yadda za a dinga yi wa mace.

Wannan layi ne

Su kuma 'yan mata wace irin tarbiyya suke so a tattare da namiji?

Wata matashiya mai suna Fatima Sanusi ta ce ba ta son namiji mai sanya wando a kasan kugu. Ba ta son mai yawan surutu duk inda ya shiga bakinsa ba burki.

Ba ta son mai zagin mutane da rashin ganin girmansu ko da a shafukan sada zumunta ne. Ba ta son wanda duk inda ya shiga da an ambaci sunansa kowa ya sanshi.

Ta ce ta fi son mai kamun kai, da nutsuwa da kawaici da girmama na gaba da shi da kuma tausayin na kasa da shi.

Ba ta son mai shaye-shaye da neman mata da rashin ganin mutuncin mata.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE