Yadda matasa ke zazzalo wando da ke bayyana duwawu a garin Birnin kebbi na ci gaba da zama barazana a cikin al'umma (Hotuna)


Tabarbarewar tarbiyyar matasa bangaren yadda wasu matasa ke sa wanduna da ke bayyana duwawu a waje a garin Birnin kebbi na ci gaba da zama barazana a cikin birnin mai alaka da tarihin tarbiyyar Musulunci.

Wani bincike da shafin isyaku.com ya gudanar ya nuna yadda wannan dabi'a ke ci gaba da zama ruwan dare kuma barazana ga asasin tarbiyyar da Iyaye da Malamansu na Makarantun Boko da na Arabiyya suka ba matasa a birnin.

Binciken ya gano cewa ba wani dalili ne ke sa matasa irin wannan hali ba face koyi da al'adun kasashen ketare da suka ci karo da tarbiyyar Islama da al'adun Hausa.

Kazalika binciken ya ce akalla yaro 3 cikin 15 a garin Birnin kebbi sukan yi amfani da irin wadannan dinkakkun wanduna, ko kuma su zazzalo wandonsu, har da na zariya dinkin Kaftani matukar suna cikin abokansu domin nuna birgewa da tunanin wayewa.

Sai dai rahotun ya gano wannan dabi'a na illa a cikin al'umma, musammmn yadda samari da ke sanye da irin wadannan wanduna ke cudani da jama'a a wajen lamurran hukuma da ke samar da cudanin jama'a don ci ma wata ka'ida ta mahukunta, ciki har da mata ba tare da jin kunya ba, kuma babu wanda ke tsawatawa nan take.

Kazalika ya bayyana a rahotun cewa wannan matsala bata tsaya a garin Birnin kebbi kadai ba. Matsala ce da ta shafin matasan arewa har da kudancin Najeriya na wannan zubin gurbin matasa, da ke kallon yin haka a zaman wata dabi'a ta nuna wayewa.

Wa ke da alhalin kula da wannan lamari?

Shafin isyaku.com na kira ga Majalisar mai Martaba sarkin  Gwandu da hukumar Hisbah na jihar Kebbi, tare da wasu Kungiyoyin al'umma da na addini, tare da jama'ar unguwanni su sa ido sosai domin ganin wannan dabi'a ta zo karshe a tasakanin matasa a jihar Kebbi.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN