Rundunar yansandan jihar Katsina ta kama wasu mata uku da ke safarar man fetur ga yan bindiga a cikin gandun dajin jihar.
Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito cewa, Kakakin hukumar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya gabatar da matan ga manema labarai ranar Alhamis 23 ga watan Satumba. Ya ce jami'an yansanda masu yawon sintiri ne suka kama su a hanyar Katsina zuwa garin Jibia.
Wadanda aka kama su ne Dija Umar, 50; Ummah Bello, 45; da Nusaiba Muhammad, 16, dukkansu suna zaune a rukunin gidajen Malali da ke karamar hukumar Katsina a jihar Katsina.
Rubuta ra ayin ka