Yadda Karnuka suka kashe karamin yaro mai shekara 2 a makaranta


Karnuka sun hallaka wani yaro dan shekara biyu a wata makaranta dake garin Amokpo dake karamar Hukumar Oyi a jihar Anambra, karnuka da yawansu ya kai 10 sun daka wa yaron warwaso ne a yayin da iyayenshi suka kaishe wata makaranta mai suna ‘Global Growth Academy’ don saka shi a makarantar, suna tsaka da cika takardun yaron ya fito inda a take karnukan mallakin mai makarantar suka cakumeshi sai dakinsu inda suka yi kaca-kaca da yaron.

‘Yan sintirin kauyen sun harbe karnuka a take, inda suka banka musu wuta, su kuwa iyayen yaran da suke karatu a makarantar suka yi maza da jin labarin suka kwashe dukkan ‘ya’yansu daga makarantar wacce wani mazaunin kasar Ingila. Dattawan kauyen Amokpo sun gargadi mutumin cewar a al’adarsu ba a kiwon karnuka a garin, amma mutumin ya yi kunnen uwar-shegu da gargadin dattawan, inda ya zuba karnuka har 10 a harabar makarantar tashi. Dattawan sun ce sun goyi bayan matakin da matasan ‘yan sintiri suka dauka na kashe karnukan.

Sarkin kauyen ya ce; sai da muka ja wa mutumin kunne, cewar bama kiwon karnuka anan garin, amma ya yi biris da jan kunnenmu, don haka kamar yadda dokar al’ummar mu ta tana da wannan mutumin ya yi kisan kai, kuma tuni mun mikashi ga hukumomi don daukar matakin da ya dace a kan mutumin, kuma zamu bibiyi lamarin don tabbatar da an yi adalci ga iyayen yaron da karnukan suka hallaka.

Leadership Hausa

Previous Post Next Post