Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta


Akalla ‘yan sanda uku aka kashe a garin Onitsha, jihar Anambra sakamakon harin 'yan bindiga.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ukaegbu/Ezeiweka a Onitsha a safiyar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

An kuma kona wata motar sintiri kurmus ta jami'an da suka mutu.

Wakilin Daily trust ya tattaro cewa wasu ‘yan sanda biyu sun jikkata a harin.

Wani ganau ya tabbatar da faruwar lamarin amma jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda na jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce har yanzu ba a sanar da shi ba batun ba.

Ana ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro a Kudu maso Gabas, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dama na 'yan sanda.

Rundunar ‘yan sandan ta zargi haramtacciyar kungiyar ta'addanci ta IPOB da kai wasu hare-hare a yankunan.

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.

Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.

Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.

An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.

Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

Mazauna a Sokoto sun hallaka 'yan ta'adda 6, sun kone gawarwakinsu kurmus

Akalla 'yan ta'adda shida, wadanda aka fi sani da 'yan fashin daji, mazauna kauye suka kashe a garin Tangaza na jihar Sokoto, Daily Nigerian ta ruwaito.

An rahoto cewa 'yan ta'addan sun sace mutane biyu a garin tare da yin watsi da tayin kudin fansa a makon da ya gabata.

Bayanai sun ce, duk da haka, 'yan ta'addan sun dage kan cewa sai sun kashe wadanda suka sacen don daukar fansa kan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa a maboyarsu, kuma sun yi hakan.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN