Da duminsa: an kori yansanda biyu daga aiki, duba abin da suka yi wa mai Keke Napep


Rundunar yansandan jihar Delta ta sanar da koran yansanda biyu da suka yi wa mai tuka Keke Napep duka suka yi masa mumunan lahani da ya kare kashin kansa. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Wadanda aka kora sune Sgt Felix Ebikabowei da Ndubuisi Abazie. Wadanda aka kora sun je aiki ba tare da izini ba bayan sun tashi daga aikin yansanda, kuma suka yi wa mai Keke lahani bayan sun yi masa dukan fitar hankali sakamakon wata gardama.

Kakakin yansandan jihar Delta  DSP Bright Edafe, ya sanar da haka wa manema labarai . Ya ce yansandan da aka kora suna aiki ne a sashe na B a ofishin yansanda da ke Warri. Ya ce bayan korar su daga aikin dansanda za a gurfanar da su a gaban Kotu.


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari