Type Here to Get Search Results !

Wasu mugaye sun kashe mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf


A wani harin mayar da martani, wasu mutane da ba a san ko su waye ba a kauyen Kacecere da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna sun halaka rayuka takwas, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, a wata takarda da ya fitar, ya ce wannan harin mayar da martani ne wanda aka fara a kauyen Jankasa da ke karamar hukumar Zangon Kataf inda aka kashe wani Yakubu Danjuma tare da halaka wasu mutum 34 da ke Madamai a karamar hukumar Kaura ta jihar.

Farmakin da aka kai wuraren nan biyu, jami'an tsaro sun gano cewa shi ya janyo farmakin mayar da martani da wasu suka kai yankin Kacecere wanda ya bar rayuka takwas a mace, mutum shida da raunika da kuma gidaje da aka kone," Aruwan yace.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa da alhini kan rahotannin kuma ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Gwamnan ya yi kira ga hukumomin da suka dace da su tabbatar da an dauka dokar gaggawa tare da yin kira ga yankunan da su guji kai harin martani .

Ya kara da kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da sun binciki lamarin, Daily Nigerian ta wallafa.

A yayin rubuta wannan rahoton, dakarun soji da jami'an 'yan sanda suna aiki a wurare daban-daban kuma za su sanar da jama'a cigaban da aka samu.

Legit Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies