Cinkoson marasa lafiya masu son ganin Likita a Asibitin Sir Yahaya na zama barazana ga lafiya - Rahotu


Duk da fice da Asibitin tunawa da Sarki Sir Yahaya ta yi na samar da jajirtattun Likitoci masu kuzari da aiki tukuru. Kazalika Asibitin ta yi give kan tsabtar muhalli. Sai dai cinkoson marasa lafiya a sashen kula da marasa lafiya na MOPD yana ci gaba da zama barazana da kalubale ga lafiyar jama'a da ke zama kafin su gan Likita.

Wani bincike da shafin labarai na isyaku.com ya gudanar, ya gano yadda yawan jama'a marasa lafiya ya karu a makonni uku da suka gabata. Sakamakon haka kujerun zama da marasa lafiya za su zauna a kai lokacin jiran ganin Likita sun yi kadan, bisa yawan adadin marasa lafiya da suka bayyana.

Kazalika, fankokin wannan sashen na jiran ganin Likita MOPD, ƙwaya daya ne kadai yake aiki a bangaren Mata, yayin da ba fanka ko daya da ke aiki a bangaren maza.


Sakamakon karancin wajen zama, marasa lafiya kan kasance a tsaye, wasu sukan zauna a kasa, wasu kuma sukan kwanta a siminti ne idan rashin lafiyarsu ta yi tsanani kafin su gan Likita.

Sai dai binciken mu, har ila yau, ya nuna cewa marasa lafiya na alfahari da Likitoci da masu jinya (Nurses) da ke kula da su a MOPD, saboda saukin kai da kulawa.

Kira ga Dr. Aminu Bunza da Gwamnatin jihar Kebbi.

Shafin labarai na isyaku.com na kira ga shugaban Asibitin tunawa da Sarki Yahaya Dr Aminu Bunza, ya kara ba da kulawa ta musaman domin ganin an inganta sashen da marasa lafiya ke zama domin jira, kafin su gan Likita.


1. A wadatar da isassun kujeri ko da benci ne.

2. A samar da fankoki masu aiki ko a gyara wadanda ake da su.

3. A samar da daya daga cikin dogarawan tsaro (Security) na Asibitin ya sa ido wajen ganin ana bin dokar tsabta a yayin da marasa lafiya ke jiran ganin Likita a MOPD.

4. A sa ido tare da tabbatar da cewa masu lalurar cutar tari sun sa takunkimin fuska kuma sun rufe hanci da baki lokacin da suke zaman jiran ganin Likita a MOPD.

5. A kara inganta tsabtar MOPD ta hanyar wanke simintin da Dettol kullum kafin jama'a su fara isowa domin ganin Likita.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN