Duba yadda sojojin Nijar suka ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto


Dakarun sojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 wadanda suka tsere yayin da 'yan bindigan daji suka far musu a Sokoto.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa an ceci sojin Najeriyan a Basira, wani kauye da ke kan iyaka karkashin yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin guiwa na sojoji da ke sansanin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami'an tsaro.

Yan bindigaan sun kai farmaki Gawata da wasu kauyuka da ke yankin.

Duk da an kai farmakin a sa'o'in farko na ranar Juma'a, ba a samu bayanai ba har sai ranar Lahadi saboda datse layikan sadarwa a jihar Zamfara da wasu sassan Sokoto da Katsina.

Dan majalisar jihar Sokoto a matakin jiha, Aminu AlMustapha Gobir, ya tabbatar da farmakin inda yace jami'an tsaro 12 sun rasa ransu.

Hakazalika, kwamishinan tsaro na jihar, Kanal Garba Moyi mai ritaya, ya tabbatar da harin ga Daily Trust amma ya ce bai san yawan wadanda aka rasa ba.

Daily Trust ta tattaro cewa, miyagun 'yan bindigan da suka kai farmakin sun hada da na kungiyoyi biyu na jiga-jigan 'yan bindigar Zamfara irin su Halilu Sububu da Kachalla Turji

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN