Wani Mai Motar Alfarma Ya Shararawa Ɗan Keke Nafef Mari Kan N500, Mutumin Ya Mutu


Wani direban motar alfarma wadda harsashi baya ratsa ta, Kayode Oluwatomi, ya laƙaɗawa ɗan nafef, Kola Adeyemi, duka har ya mutu a Ilorin jihar Kwara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa direban Nafef ɗin ya buga wa mutumin, lamarin da ya jawo lalacewar fitilar yin fakin.

Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a yankin Gerin Alimi, cikin garin Ilorin.

Mai Nafef, Adeyemi, ya bugi motar ta alfarma mai lamba BX 954 AJL a baya, lamarin da ya jawo fasa fitilar aje mota, wanda ake siyarwa N2,500.

Shin ɗan nafef din ya biya kuɗin?

Wani shaidan gani da ido, wanda ya ɓoye sunansa, yace direban nafef ya roki alfarma zai biya N2,000 na ɓarnar da yayi, amma mai motar yaƙi amincewa.

Mutumin yace:

"Nan take rikici ya ɓarke tsakaninsu, mai motar ya ɗaga hannu ya mari ɗan nafef ɗin da wani abu da ake zargin zobe ne ko laya, nan take ya faɗi kasa warwas."

"Daga baya an tabbatar da ɗan nafef ɗin ya rigamu gidan gaskiya a asibitin Garin Alimi dake Ilorin."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Yace mataimakin shugaban ƙungiyar direbobin keke nafef, Ganiyu Adebayo, ya kawo wa yan sanda rahoton yadda lamarin ya faru tsakanin mai motar da kuma ɗan nafef.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN