-->

Ads

Duba mumunar barna da jirgin yakin soji ya yi kan bayin Allah cikin kuskure a jihar Yobe

Duba mumunar barna da jirgin yakin soji ya yi kan bayin Allah cikin kuskure a jihar Yobe


A Najeriya, bayanai na ƙara fitowa fili kan yadda wani jirgin sama ya yi ɓarin wuta a ƙauyen Buhari cikin ƙaramar hukumar Yunusari a jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar.

Shaidu sun ce harin jirgin saman ya yi sanadin kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata cikinsu har da mata da ƙananan yara a yankin na arewa maso gabashin ƙasar.

Wani mutum da lamarin ya yi sanadin mutuwar danginsa takwas ya ce jirgin yaƙin ya harba makami fiye ɗaya a kan gidajen mutane.

Ya kara da cewa wadanda lamarin ya shafa ko dai su na shirin zuwa kasuwa ne, ko gona ko wadanda ke zaune a cikin gida su na gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

''Jirgin ya zo daga gabas ya na ta barin wuta sai kuma ya yi yamma, daga nan sai ya yi kudu ya na ta zuba wuta babu kakkautawa. Lamarin ya shafi kanin babana, akwai kakana da matar babana da sauran yaransu kanana, 'yan uwana kadai sun kai takwas. Mun kawo su asibiti cikin gaggawa, ana yi musu magani ,wadanda suka mutu kuma an binne su. Mun je mun kai rahoto ga shugaban karamar hukumarmu kuma sun kawo ma na taimakon gaggawa,'' inji Alhaji Ali Lawan.

Alhaji Ali, ya ce lamarin ya faru ne da safe kowa ya na gani, kuma sun tabbatar da cewa jirgin sojoji ne saboda ya yi kasa-kasa sannan mutane sun gan shi da idonsu, an kuma cire wa wadanda abin ya shafa albarusai da karafa. Sannan mutane na fadin launin fentin jirgin irin na kakin soji ne, wasu na cewa launin ruwan toka ne.

'Wani jirgin yaki ya yi barin wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama'

Sojojin Najeriya sun musanta binne gawawwakin ƴan bindiga a manyan ƙaburbura a Zamfara

An kubutar da daliban makarantar Kayar Maradun a Zamfara

Ya ce,''Wadanda suka ji munanan raunuka ni da kai na ne na yanka musu takardar asibiti su 20, kuma yara kananan da suka ji ciwo aka za a wuce da su babban asibiti da ke Maiduguri. Ya yin da wadanda suka rasu kuma mutum takwas.''

Daga bisani daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani bangaren garin, kamar yadda wani da 'yan uwansa suka mutu a lamarin ya shaida wa BBC.

BBC ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Yobe inda kakakinta ASP Dungus Abdurrahman, ya ce ba su samu labarin ba, amma za su tuntubi BBC idan suka samu labarin.

Sai dai kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya musanta yin ɓarin wuta a cikin wata sanarwa da ya fitar.

"Rundunar sojin sama ta gudanar da aikinta na karshe a jihar Yobe (ba a karamar hukumar Yunusari ba) a ranar 5 ga watan Satumban 2021, kuma bincike aka yi ya nuna cewa ba a saki bam ko makami mai linzami ba," in ji sanarwar.

BBC Hausa

0 Response to "Duba mumunar barna da jirgin yakin soji ya yi kan bayin Allah cikin kuskure a jihar Yobe"

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN