Mawakin Iran da zai iya shan dauri kan saka mata Turawa a wakarsa


Mawakin kasar Iran Mehdi Rajabian, zai fuskanci zaman gidan yari kan yin wata waka.

Ya riga ya shafe shekaru biyu a tsare - hadi da kadaice kansa da kuma yajin cin abinci - sakamakon sakin wakokin da mahukuntan Iran ba su amince da su ba. Amma ya jajirce.

''Ba zan ja da baya ba kuma ba zan tantance kai na ba,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Haka kuma, ya jima yana aiki a boye daga wani dakinsa na karkashin kasa a gidansa da ke Sari, a arewacin kasar Iran, don fitar da sabuwar waka.

Wacce aka yi wa take da 'Coup Of The Gods', wakar ta kunshi kungiyar mawaka ta kasar Brazil, tare da mawaka daga kasashen Turkiya da Rasha da Indiya da Argentina da kuma mawaka mata biyu daga Amurka, Lizzy O'Very da Aubrey Johnson.

Wadannan muryoyi sun kara wa wakokin Rajabian na bakin-ciki da gwagwarmaya armashi. Amma kuma suna kunshe da wasu kausasan kalamai na siyasa - saboda an haramta saka muryoyin mawaka mata a kasar Iran.

Lokacin da Rajabian ya sanar da aniyarsa ta aiki tare da mata mawaka a shekarar da ta gabata, an cafke shi aka gurfanar da shi a gaban kotu, inda alkalin ya shaida masa cewa ''yana karfafa yin karuwanci''.

Bayan da aka yi belinsa, ya ci gaba da hada wakokinsa, duk kuwa da barazanar daure shi a gidan yari da ake yi.

Yanzu na kammala wakokin,''yanzu za su sake zargina'', kamar yadda ya shaida wa BBC,. ''Babu ko tantama a kai. Amma ba zan ja da baya ba.

"Abin takaici ne a ce a irin wannan zamanin muna maganar haramcin wakoki.''

Yajin cin abinci

Rajabian ya fara fuskantar matsaloli a shekarar 2013, lokacin da dakarun juyin juya hali suka kai samame ofishinsa, suka rufe wurin da yake shirya wakokin kuma suka kwashe na'urorinsa.

A can baya yana amfani da wani suna da ke da'awar mata mawaka kuma yana aiki kan wakokin. Tarihin Iran daga Setar, wanda ya bayyana ya shafi abin ya faru a yakin Iran da Iraqi.

An zarge shi da rarraba ''wakokin da ya hada a boye, da dama da suka kunshi kalmomi da sakonnin da ba su yi wa mahukuntan kasar Iran ko addinin kasar dadi ba,'' aka kulle shi a gidan yari.

Rajabian ya ce ya shafe kwanaki 90 a tsare a kuma kadaice, tare da rufe masa idanu ta yadda ba zai iya sanin da abubuwan da ke kewaye da shi ba.

Daga bisani ne aka bayar da shibeli, amma an sake cafke shi a shekarar 2015 - a wancan karon tare da dan uwansa mai shirya fina-finai, Hossein Rajabian - aka yanke musu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, bayan shari'ar minti uku.

Saboda nuna rashin jin dadi, duka 'yan uwan junan suka shiga yajin cin abinci har na tsawon kwanaki 40 days.

Rajabian ya ce nauyinsa ya ragu da kilo 15, kuma ya rika yin aman jini.

Abubuwan da ya fuskanta suna kara karfafa bude hanyar shirya sabuwar waka, mai taken "The Whip On A Lifeless Body."

''A rana ta 19 ta yajin cin abincin, na bude idanuna kuma ban san ko a mace nake ko a raye ba, a duniya nake ko a lahira. Na shiga wani hali na gushewar hankali. Wani irin yanayi ne."

Yajin cin abinci ya kuma sa gabobin Rajabian sun kumbura, hakan na nufin ba zai iya yin waka da kan sa ba.

A maimakon haka, ya hada wakokinsa ya tura wa mawaka masu tausaya masa a fadin duniya.

Sun shirya na su bangaren suka sake tura masa zuwa kasar Iran, inda ya sake harhada wakokin wuri guda, cikin fama da matsalar rashin karfin intanet da kuma sa idon da mahukuntan Iran ke yi akan sa.

Shugaban makarantar koyon shirya wakoki Harvey Mason Jr (daga dama, tare da John Legend) ya taimaka wajen kammala wakar

Wani mai shirya wakoki BaAmurke Harvey Mason Jr wanda ya taba rubutawa tare da hada waka da mawaka irin su Aretha Franklin da Michael Jackson da Beyoncé da kuma Britney Spears ne ya hada tare da sarrafa wakokin.

"A lokacin da na fara magana da Mehdi na ji sha'awar batun, daga nan ne lokacin da na ji labarinsa ya kara ba ni sha'awa,'' kamar yadda ya ya shaida wa BBC. ''Daga karshe lokacin da na saurari wakar, na ji wani irin dadi.

"Mehdi ya yi wani abu mai jan hankali da kuma kyau a cikin wani yanayi matsananci.''

'Makamin fadin gaskiya'

Ana sa ran wakokin za su fita a ranar Juma'a, kuma hakan na zuwa ne makonni bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki a Afghanistan makwabciyar kasar Iran.

Tuni dai sabuwar gwamnatin ta haramta saka wakoki a bainar jama'a, da suka kira a matsayin ''haramun a addinin Musulunci''; yayin da dakarun Taliban suka harbe mawakin gargajiya Fawad Andarabi bayan da suka janyo shi daga cikin gidansa.

Rajabian ya bayyana cewa jajircewa ce kadai magani.

"A yankin Gabas ta Tsakiya, kayan kida kan zama wani makami mai karfi kamar bindiga,'' kamar yadda ya shaida wa BBC lokacin da a karon farko ya sanar da wakarsa a cikin watan Janairun shekarar 2020.

A yanzu ya ce: "Wata rana, mutane za su tuna baya su fahimci cewa ba waka kadai muke yi ba. Mun samar da ilimin falsafa da tunani mai zurfi game da rayuwar bil'adama ta hanyar waka.

"Yin shiru game da zalunci tamkar hada kai ne da masu zalunci. Ba zan taba yin shiru ba, Waka ta ita kadai ce makamin gaskiya, na jajirce wa duk wani camfi.''

A yayin da ba za a rika sauraron wakokin Rajabian a kasarsa ba, yana cike da fatan mutane a wasu kasashen za su rungume wakokin da kuma sakonnin tausayi da karfafa gwiwa.

"Muddin mutane za su saurari wakokina su kuma rika bibiya ta, zai taimaka min kasancewa a raye, ba a tauye muryata ba,'' in ji shi.

"Za iya shaida wa duniya cewa babu wani mulkin danniya da zai hana 'yancin yin waka. Na fuskanci duka haramci da kuma kasancewa a gidan yari, kuma a yau na fitar da sabbin wakoki ga masu sauraro. Ko da kuwa zan kare a tsare.''

BBC hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN