Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya magantu kan wani muhimmin lamari game da Najeriya


Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya ce Najeriya ta rasa kimarta a matsayin uwa a Afirka ga sauran kasashen da suka bunkasa tattalin arzikin su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanusi ya ce yanzu Najeriya tana bayan sauran wasu kasashen Afirka da yawa idan aka duba ta fuskar ci gaba.

Sanusi wanda ya kasance Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya fadi haka ne a yayin rufe taron Babban Taron Zuba hannun Jari na Kaduna, mai taken, ‘KadInvest 6.0.’

Ya ce yayin da Najeriya ke dogaro da danyen man fetur, wanda ke kan gabar karewa da kuma wahalar siyarwa, sauran kasashen duniya na rungumar harkar fasaha.

A kalamansa, cewa yayi:

“A duniya, ana sake fasalta aiki; Kashi 30 zuwa 40 cikin dari na ma’aikata a kasashen da suka ci gaba za su bukaci inganta hazakar basirarsu nan da 2030. Kuma mene ne manyan dalilan wannan sake fasalin? ICT da aiki daga nesa, wanda muka gani ko a nan yayin COVID-19.

Sanusi ya kuma bayyanacewa, nan da wani lokaci, ayyuka za su ragu kasancewar karuwar fasahar mutum-mutumi da ake yi a duniya wanda zai bar wasu 'yan Najeriya da basu san yadda ake sarrafa mutum-mutumi cikin yanayi na rashin aikin yi.

Da yake magana kan yadda tattalin arzikin ya zama tsohon yayi, Sanusi ya ce:

“A gare mu a Najeriya, tattalin arzikin da muke da shi, abin da ake kira akwakwar da ke yin kwan zinare tana gab da mutuwa. Ba za ta sami kwan ba. Ci gaba ba ta ta'allaka da sinadarin carbon ba.

"Yan watanni da suka gabata, Jamus ta sami damar samar da isasshen makamashi mai sabuntawa ga duk bukatun kasar.

"A yau, muna fuskantar matsaloli wajen sayar da man Najeriya. Don haka, ba wai kawai muna samun matsalolin samarwa bane, koda mun samar, sayarwa ma aiki ne.

“Don haka, wannan yana tilasta canji, kuma a gare mu, kasar da ta dogara da mai, abubuwa na bukatar canzawa.

“Najeriya tana kan matsayi na 114 a cikin jerin kasashe masu kirkira a duniya. Mun yi kasa da sauran kasashen Afirka kamar Kanya, Rwanda da Senegal. Karshe ma, muna matsayi na 14 a yankin kuduncin Sahara na Afirka.

"Ina ganin ya kamata mu yi wannan duba na gaskiya kuma mu san inda muke a matsayin kasa. Ya kanta mu daina kiran kanmu uwa a Afirka saboda mu kato ne da kafafu duk yumbu."

Legit Nigerian

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN