Type Here to Get Search Results !

Gwamnatin Kano ta nada sabon sarkin Gaya


Gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta nada Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon sarkin Gaya.

Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji kuma wazirin Gaya kuma shugaban masu zaben sarkin Gaya ne ya sanar da nadin sabon sarkin a ranar Lahadi.

"Dokar masarautar Kano ta 2020 ta amince da nadin Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya a matsayin sabon sarkin Gaya," kamar yadda ya bayyana a sanarwar.

An nada sabon sarkin ne bayan rasuwar Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir a makon da ya gabata.

Sarki Ibrahim Abdulkadir ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Sarkin ya rasu yana da shekara 91, kuma ya shafe shekara 30 yana kan karagar mulki.

A shekarar 2020 ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da Sarkin Gaya mai daraja ta farko, tare da na wasu masaratun uku a jihar Kano.

Sabon Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir dan Marigayi Sarkin Gaya ne Alhaji Ibrahim Abdulƙadir. Kuma shi ne dansa na biyu

Kafin Naɗin sa dai shi ne Chiroman Gaya.

BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies