Type Here to Get Search Results !

Wani saurayi ya sheke tare da gundule kan kaninsa mai shekara 14 domin yin tsafin samun kudi da dukiya


Rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC reshen jihar Kwara ta kama wani saurayi mai shekara 25 da haihuwa mai suna Ismail Saliu, bayan ya hada baki da wasu ya yi wa kaninsa mai suna Azeez Saliu yankan rago saboda dalilan tsafi don samun kudi.

Kakakin rundunar NSCDC a jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya sanar war manema labarai a wata Takarda da ya fitar ranar Asabar 25 ga watan Satumba.Ya ce lamarin ya faru ne a garin Kosubosu, da ke karamar hukumar Baruten.

Ya ce jami'an rundunar ne suka kama wani mai maganin gargajiya mai suna Ahmed Nkwe, 44, lsmaila Saliu 25, da Saliu Ahmed, 30”.

Ya ce sakamakon binciken rundunar ya nuna cewa yayan Azeez mai suna Ismail Saliu ne ya ja kaninsa zuwa wani daji. Inda ya hadu da mai maganin gargajiya Ahmed tare da Saliu suka kashe Azeez Dan shekara 14 kanin Ismail mai shekara 25.

Binciken ya nuna cewa Ismail ne da hannunsa ya yanke kan kaninsa daga gangar jikinsa.

Asirin su ya tonu ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga gonar da suka yi aika-aikar, sai jami'an sashen Anti Vandal na NSCDC suka cafke su kuma bayan gudanar da takaitaccen binciken abin da suka dauko sai aka gan kan Azeez a kayakin su.

Kwamandan rundunar NSCDC na jihar, lskil Makinde, ya bayar da umarnin mika matsalar ga Shelkwatar yansandan jihar Kwara domin gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin da kuma fuskantar tuhuma. 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies