Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara


Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.

A cewarsa:

“Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta sanya dole a kkatse dukkan ayyukan sadarwa a jihar daga yau 03 ga Satumba, 2021.

"Wannan zai baiwa hukumomin tsaro da suka dace damar aiwatar da ayyukan da ake bukata don magance kalubalen tsaro a jihar, daidai da bukatun, an umarci Globacom da ta rufe dukkan shafuka a jihar Zamfara da kowane rukunin yanar gizo a cikin makwabciyar jihar da za ta iya bayar da sabis na sadarwa a jihar Zamfara.

“Rufe shafin na sati biyu ne (03 ga Satumba - 17, 2021) a matakin farko. Ana bukatar daukar matakin gaggawa a wannan batun.”

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Jami’an tsaro na rundunar ‘yan sanda sun cafke wani dan bindiga da ake zargin yana cikin ‘yan bindigan da suka afkawa Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Afaka da ke Jihar Kaduna a cikin watan Maris.

Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin wadanda suka kitsa kuma suka kashe akalla mutane hudu da suka sace daga cikin dalibai 37 na kwalejin a ranar 11 ga Maris 2021.

An saki daliban bayan kwanaki 55 da aka yi garkuwa da su kuma an biya kimanin Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaro sun afkawa al’ummar Askolaye da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu a ranar Lahadin da ta gabata bayan sun bi diddigin wanda ake zargin na tsawon makwanni.

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin, Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN