Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger



Jami'an rundunar yaki da 'yan bindiga ta 'yan sandan jihar Niger sun bindige gagararren mai kai wa 'yan bindiga bayanai, Buba Baromi.

An sheke Baromi ne a wata maboyarsa da ke dajin Damba na jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger. Hoto daga Vanguardngr.com

PRNigeria ta tattaro cewa, wasu mafarautan yankin sun jagoranci 'yan sanda maboyar Baromi inda ya ke jinyar wani harbin bindiga da aka yi masa yayin wata arangama da yayi da jami'an tsaro a baya.

Wani jami'in sirri da aka yi aikin da shi, ya sanar da PRNigeria cewa, Baromi ba bayanai kadai yake kai wa 'yan bindiga ba, har jagorantarsu yake yi zuwa wurin da za su kai farmaki kuma su sace jama'a.

"Shehu Buba Baromi gagararren mutum ne da ke samarwa da miyagun 'yan bindiga bayanai tare da jagorantarsu zuwa inda za su kai farmaki, su sace jama'a ko kuma satar shanun jama'a.

“A tsakiyar watan Augusta, ya jagoranci wasu miyagu masu satar shanu kuma sun kaddamar da hari a kauyen Dogon Fadama inda mutane suka rasa rayukansu.

“A wata arangama da 'yan sanda da yayi, ya samu rauni daga harsashi kuma ya tsere zuwa dajin Damba inda ake jinyarsa.

“Amma kuma, a ranar Talata, 'yan sanda sun tsinkayi dajin kuma sun yi musayar wuta da 'yan bindiga da ke jinyarsa, lamarin da yasa aka sheke shi a take.

“An adana gawarsa a wani asibiti saboda wadanda ya cutar da wadanda suka san gagararsa su tabbatar da mutuwarsa," yace.

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

A wani labari na daban, shugabannin jam'iyya mai mulki ta APC, sun ce kusan makuden kudi da suka kai tiriliyan daya da kadarori shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwato daga mahandama bayan hawansa kujerarsa a APC, Daily Trust ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Alhamis, tsohon sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu, mamba na kwamitin rikon kwarya, Barista Isma'il Ahmed, hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi da darakta janar na zauren gwamnonin jam'iyyar, Salihu Lukman, sun ce an samu manyan nasarori.

Kamar yadda takardar ta shaida, gwamnati ta na amfani da kudaden da ta gano ne wurin ayyuka na musamman da kuma sanya hannun jari ko kuma a shigar da su cikin kasafin ko wacce shekara.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN