Yadda mata biyar suka bayyana rayuwa a karkashin tsarin shari'ar Musulunci a wasu sassan duniya


Zango na farko na mulkin Taliban ya kasance cike da cin zali da danne hakkin mata, wadanda aka tsame su daga harkar neman ilimi da aiki, da ma dukkan wasu aikace aikacen jama'a.

Sai dai a wannan karon, ƙungiyar ta ce za a tafi da mata, za a mutunta 'yancinsu bisa tsarin Shari'ar Musulunci, sai dai baza a iya cewa ga yadda al'amura za su kaya ba.

A ƙashin gaskiya, Shari'a tsarin zamantakewa ne bisa umarnin Ubangiji, ciki har da Sallah da azumi da sadaka ga mabukata

Haka kuma wani tsari ne na shari'a, inda ake hukunta masu laifi dai dai da ka'idar addinin Islama, amma wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a na ganin baiken tanaje-tanajen hukunci bisa tsarin shari'ar Musulunci a wurare da dama.

Ko da yake akwai iyakar da aka yi wa mata ta fuskar shiga siyasa a tsarin shari'ar Musulunci, sai dai kasashe da dama da ke bin tsarin shari'ar Musulunci ba sa tsauwalawa kamar yadda Taliban ta yi a Afghanistan a shekarun 1990.

BBC ta tattauna da wasu mata biyar kan yadda rayuwarsu ke kasancewa karkashin tsarin shari'ar Musulunci a kasashen Saudiyya da Najeriya da Indonesia da Brunei.

'Kasa ce mai cike da 'yanci sosai'

Hannan Abubakar

ASALIN HOTON,HANNAN ABUBAKAR

Bayanan hoto,

Hannan ta ce tana cike da farin ciki sakamakon sauyin da aka samu a Saudiyya

Ni 'yar asalin ƙasar Tanzaniya ce, sai dai mafi yawan rayuwata na yi ta ne a Saudiyya, in ji Hannan Abubakar.

Na je wata makaranar kasa da kasa da a ke koyar da dalibanta bisa tsarin koyarwar Indiya.

A cikin motocin bas, yara maza da mata kan zauna daban-daban, yayin da a kantuna kuwa ake ware wajen maza daban na mata ma daban.

Su kansu azuzuwanmu ma na mata daban suke da na maza, sai dai duk da haka malamai maza ne ke koyar da mu a wasu fannoni.

An bai wa 'yan mata damar shiga wasanni, amma ba tare da samari ba, kuma mukan yi bikin wasanninmu a ranakun da suka sha bamban don gudun cakuduwa maza da mata.

Hannan Abubakar tare da abokanta

ASALIN HOTON,HANNAN ABUBAKAR

Bayanan hoto,

Hannan, wadda ita ce ta karshe a bangaren hagu a wannan hoton, ta ce yanzu ba wajibi ba ne rufe fuska a audiyya

Saudiyya ta kasance wuri mai 'yanci a yanzu. Mata za su iya tafiya su kaɗai kuma su tuƙa motoci. Ina shirin samun lasisi nan ba da jimawa ba.

Bayan 'yan shekarun baya ba mu da sinimomi, amma yanzu muna da su kuma muna zuwa, ina son zuwa irin wadannan wurare.

Ba na rufe fuskata kuma ba "dole" ne sanya mayafi ba.

A da, gidajen cin abinci suna da bangaren iyalai daban. Yanzu ba mu da irin wannan wariya. A wuraren taruwar jama'a, maza da mata za su iya haduwa, alal misali ina fita cin abinci tare da abokan aikina maza.

Hannan na zuwa Sinima da danginta da abokanta

ASALIN HOTON,HANNAN ABUBAKAR

Bayanan hoto,

Hannan na zuwa Sinima da danginta da abokanta

'Haramun ne shan barasa, amma ana sha a wuraren holewa'

Sai dai duk da haka har yanzu ƙasa ce ta Musulmai, don haka babu kulob na dare, ba mashaya da sauransu. Ba a yarda da giya ba.

Ina aiki a kamfanoni masu zaman kansu a Jidda. A cikin kamfanina, ana biyan mutane gwargwadon aikinsu ba don jinsi ba.

Shekaruna 30; Zan yi aure lokacin da na hadu da kyakkyawan sahibina. Ina da iyayen da suke ƙarfafa mini gwiwa sosai, ba sa tilasta mini in yi aure.

Wasu na cewa wadannan sauye-sauye sun zo a makare, amma mahaifiyata da ta kasance a Saudiyya tun kafin a haife ni ta ce ta ga saurinsu.

Mahsa na rubutu

ASALIN HOTON,MAHSA

Bayanan hoto,

Mahsa ta ce 'yancin mace a Iran ya ta'allaka ne a kan arzikin ahalinta

A Iran, irin takunkumin da mace ke fuskanta ya danganta da asalin danginta in ji Mahsa. (Mahsa ta nemi kar a yi amfani da cikakken sunanta ko nuna fuskarta don tsaron lafiyarta.)

Ana iya raba al'ummar Iran gida uku. Wasu masu tsananin addini ne, da masu tsaurin ra'ayi, da masu zazzafan tunani da nuna wariya, har ma za su iya kashe 'ya'yansu mata ko' yan'uwa mata saboda wata alaƙa mai sauƙi da saurayi.

Rukuni na biyu kamar iyalina ne, masu matsakaicin ra'ayi, babban abin da suka mayar da hankali a kai shi ne samun ilimi da aiki.

Na uku kuwa su ne attajirai ne masu arziki waɗanda doka ba ta aiki a kansu.

An haife ni kuma na girma a Tehran. A makaranta da jami'a na yi karatu tare da samari.

Yawancin iyaye a Iran suna son yaransu su yi karatun likitanci ko injiniya, amma na kasa samun gurbin karatu a kwalejin koyar da aikin likitan hakora, kuma na karanci Turanci. Ina koyarwa a makarantar yara.

Mata a Iran na tafiya garuruwa daban -daban. Mata marasa aure za su iya yin hayar gida su zauna su kaɗai. Suna kuma iya shiga cikin otel da kansu.

Ina da mota tawa kuma ina zaga gari. Babu bukatar abokin rakiya namiji, amma sanya abin rufe fuska {Nikab} wajibi ne.

Mahsa in a wurin motsa jiki

ASALIN HOTON,MAHSA

Bayanan hoto,

Mahsa ta ce tana tuka motarta da kanta

Idan jami'an kiyaye shari'a suka ƙyallara ido suka hango wasu matasa na lalata ko wata mace sanye da ɗan gajeren mayafi, to kuwa za su shiga matsala. Amma za a iya barinsu su tafi idan suka bada ɗan na goro.

Wani lokaci ana iya kai masu laifin zuwa ofishin 'yan sanda kuma ana kiran iyayensu don a kunyata yaran.

"Na yi soyayya da saurayina ta tsawon shekaru hudu kafin in yi aure. Na kan je gidajen sinima, wuraren shakatawa da ko ina tare da shi.

"Na yi sa'a. Babu wanda ke tsayawa bin diddigin ko ma'aurata ne mu ko kuwa a'a.

"Iyayena suna da kafiya sosai, ko yaushe suna son in dawo gida kafin kare 9 na dare, kuma ba za su bar ni in yi tafi tafiye -tafiye tare da abokaina ba. Amma bayan aurena na samun 'yancin yin duk abin da nake so.

An haramta barasa. Ba mu da mashaya. Amma mutane suna siyan ta a ɓoye suna sha. Ni ban taɓa ko lasa ba, don bana son wannan dacin nata.

Ba na so in haifi yara, don albashinmu bai taka kara ya karya ba,

Na yi imani da Allah amma ni ba na tsauwalawa a addini, ba na yin addu'a kowace rana.

Huwaila ta ce ta nemowa mata da yawa hakkinsu

ASALIN HOTON,HUWAILA IBRAHIM MUHAMMA

Bayanan hoto,

Huwaila ta ce ta nemowa mata da yawa hakkinsu

Ni lauya ce ta shari'a kuma na yi shekaa 18 a Kano, Abuja da Legas, in ji Huwaila Ibrahim Muhammad daga Najeriya.

Na yi imani da tsarin shari'a. A cikin jihohi 12 na Najeriya, ana amfani da ita don warware laifukan da suka shafi iyali.

Ina yin aiki a kotunan shari'a da kuma kotunan shari'a na gama gari, alkalai maza ne ke jagorantar kotuna amma mata suna jayayya ba tare da tsoro ba.

Alƙali yana buƙatar yin la'akari da abubuwa da yawa na yin sassauci kafin bayar da mafi girman hukunci.

A wasu laifuffuka, ana yanke hukunci a gaban kotu amma har yanzu ban ga an hukunta mata haka ba.

Wasu hukunce-hukuncen da aka yanke na yin jifa da kisa sun sun ja hankalin duniya, amma ba a aiwatar da su ba.

Idan aka zo ga rabon gado, kason maza na ninka na mata, wannan na iya zama rashin adalci, amma akwai dalili don a baya ba a ba mata nauyin kuɗi ba. Hakkin iyaye ne, 'yan'uwa da mazaje su kare su.

'Na san abun da ya dace da wanda bai sani ba''

Huwaila ta ce ana adalci ba tare da la'akari da jinsi ba

ASALIN HOTON,HUWAILA IBRAHIM MUHAMMA

Bayanan hoto,

Huwaila ta ce ana adalci ba tare da la'akari da jinsi ba

Eh akwai dokar da ta ce mutum zai iya dukan matarsa, amma yadda fahimtar take shine miji zai dan buge ta ne amma ba yadda zai raunatata ko kuma ya illata ta ba.

Wasu mata sun gurfanar da mazajensu da ke cin zarafinsu gaban kotu. Na wakilci wasunsu da yawa, kuma na ci irin nasara a irin waɗannan shari'o'in.

Zan ce ana yin adalci ba tare da la'akari da jinsi ba.

A Najeriya ba sai kun rufe fuska ba. Mata a nan sun saba rufe jikinsu, zai zama abin ban mamaki idan wani ya sanya ɗan gajeren siket.

Hukunta mata saboda rashin sanya cikakkiyar sutura ko gyale ba daidai ba ne. Mata suna da 'yancin zaɓar abun da za su sanya a jikinsu.

Idan aka yi amfani da Shari'a kamar yadda ake tsammani, ta fi kowace doka cika.

Izzati Mohd Noor

Noor ta ce musulunci ya canja mata rayuwa

ASALIN HOTON,IZZATI MOHD NOOR

Bayanan hoto,

Noor ta ce Musulunci ya canja mata rayuwa

An haife ni kuma na girma a Brunei. Na bar ta a 2007 lokacin ina shekara 17 bayan na karɓi tallafin karatu na gwamnati zuwa Burtaniya, in ji Izzati Mohd Noor.

Na yi karatun digiri, da masters da PhD a injiniyar sinadarai a London. Bayan haka na yi aiki a bankin saka jari a matsayin mai haɓaka manhajoji.

Makonni kadan da suka gabata na dawo ƙasata. Mafi yawan mutane a nan suna bin addinin Islama. An dade ana amfani da dokokin Sharia a cikin abubuwan da suka shafi aure, saki da gado.

Mutum zai iya ganin mata sanye da abin da suke so idan ka je gidan motsa jiki, za ka ga wata da mayafi da wata sanye da rigar wasanni.

Ba mu da jami'an wanzar da shari'ar musulunci da za su hukunta mutane.

''Cikar burina''

Noor ta gamu da saurayinta yayin da take koyar tukin jirgin sama

ASALIN HOTON,IZZATI MOHD NOOR

Bayanan hoto,

Noor ta gamu da saurayinta yayin da take koyar tukin jirgin sama

Idan aka zo ga batun gado, 'yan'uwan mace maza kan samu ninkin abin da mata suke samu, kamar yadda Sharia ta tanada.

Amma a cikin ƙasarmu, yawancin mutane kamar kakannina sun bar wasiyya a kan hakan.

Ba na yin sallah sau biyar a rana kamar yadda addini ya umarce ni amma ina yin iya gwargwadon iko. Lokacin da nake ƙarama iyayena tsayayyu ne a kan addini.

Na taba samun kaina a wani lokaci da bana yin sallah ko kadan.

Na samu lasisin tukin jirgin sama a lokacin da nake karatu, a can na hadu da saurayina, shi daga arewacin Jamus yake.

Na gaya masa tun farkon dangantakarmu cewa ni mai addini ce kuma ina so iyalina su kasance kan tsarin Musulunci. Ya mutunta burina kuma ya musulunta. Za mu yi aure nan ba da jimawa ba.

Wasu malaman addinin musulunci na ganin bai kamata namiji da mace da ba addininsu daya ba su kasance tare, amma ina matukar jin cewa mutane biyu da ke son sadaukar da kansu ga aure su san juna kafin su yarda su ci gaba da rayuwarsu tare.

''Wani bangare ne na imaninmu.

Izzati Mohd Noor on a cliff

ASALIN HOTON,IZZATI MOHD NOOR

Bayanan hoto,

Noor ta ce mata da yawa a Brunei cun cimma burinsu na rayuwa

Na san abin da ke dai-dai ko abin da ba dai-dai ba bisa ga addini. Na kuma san abin da ke dai-dai da abin da ba dai-dai ba a gare ni.

Ba na sanya mayafi. Wasu ma na iya cewa ni ba Musulmar kirki ba ce. Amma a wurina, tsakanina da Allah ne, kuma idan Allah yana ganin shi ya san komai.

Neman ilimi da sabbin dabarun tafiyar da addini shine babbar darajar Musulunci.

Ban san daga ina wannan masu ra'ayin hana mata neman ilimi suka samu wannan ra'ayi nasu ba. A wurina wannan bai sabawa Musulunci ba.

Ina ƙoƙari in zama musulma ta gari a kowanne lokaci.

Nasyiratudina

ASALIN HOTON,NASYIRATU DINA

Bayanan hoto,

Nasyiratudina

Ni daliba ce mai shekaru 19, ina karantar ilimin tattalin arziki kuma ina aiki a matsayin sakatariya ga wani babban jami'i, in ji Nasyiratudina daga Indonesia. A lokacin hutuna ina koyarwa a wata makarantar yara.

An haife ni kuma na girma a Aceh Besar, Indonesiya ce ta fi yawan musulmai a duniya, amma lardin Aceh ne kawai ke ƙarƙashin Sharia.

Ina yin sallah sau biyar a rana. A gare ni, shari'a wani bangare ne na ban gaskiyarmu. Na yarda da duk sharuddanta.

Ina sanya da dogayen riguna da gyale amma ba na rufe fuskata. A nan mata ba za su iya sanya karamar riga ko gajeren wando.

Zan iya zama mai zaman kaina idan ina so. A jami'a, yara maza da mata suna karatu tare a aji ɗaya amma suna zama daban daban. Babu haramcin mu'amala da samari. Ina magana da su amma ba su da yawa.

Nasyiratudina na son ta bude makarantar kanta

ASALIN HOTON,NASIRYATU DINA

Bayanan hoto,

Nasyiratudina na son ta bude makarantar kanta

Wasu abokaina suna soyayya. Yana da kyau a kasance cikin soyayya. Samari da 'yan mata marasa aure ba sa iya fita biyu -biyu ko nuna soyayya ga junansu a bainar jama'a. Yawancin mata ba sa kusantar jukkunan junansu saboda an hana a addininmu.

Samari da 'yan mata na iya fita waje tare in ana da yawa, muna hutawa a manyan kantuna, da gidajen cin abinci.

Ba mu da dakunan sinima a nan, amma ina kallon Ina kallon fina-finai a talabijin kuma ina amfani da shafukan sada zumunta. ina son kida, don har na taba shiga wata gasar mawaka ma, inda na samu nasara na lashe ta.

A Musulunci, mutum na iya aurar mata hudu. Amma, ba zan zama matar kowa ta biyu ko ta uku ko ta huɗu ba, ba zan iya zama haka ba. Kowace mace ta cancanci mijin kanta.

Ina so in zama 'yar kasuwa, sannan in bude makarantar koyar da yara.

Ina tausaya wa matan Afghanistan. Ina fatan zan rayu tsawon lokaci don ganin dukkan mata da yaran Falasdinu, da Afganistan, da Siriya, da Iran sun farka don kwatar wa kansu 'yanci.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE