Tonon asiri: An gano wata Ma’aikaciyar jinya mai amfani da takardun bogi bayan ta yi watanni 3 tana amsar albashi


Hukumar lafiya ta jihar Legas ta kama wata Olufunke Adegbenro wacce babban asibitin Isolo na jihar Legas ya dauka aiki tun watan Yulin 2021, bisa amfani da takardun makaranta na bogi.

Punch Metro ta bayyana yadda jami’an kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kama Adegbenro a wani taro na tantance ma’aikata da su ka yi bayan ta kwashe watanni 3 tana amsar albashi daga wurin gwamnatin jihar.

Duk takardun makaranta na bogi ne

Wakilin Punch Metro ya tattaro bayanai akan yadda Adegbenro ta yi takardar digiri a karatun jinya ta jami’ar fasahar Ladoke Akintola ta bogi, takardar shaidar bautar kasa, takardar rijistar zama cikakkiyar ma’aikaciyar jinya daga kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma da kuma lasisin yin aikin jinya duk na bogi.

Shugaban NANNM na jihar Legas, Olurotimi Awojide ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce yayin da ake tantance ma’aikatan asibitin aka gano ha’incin.

Kamar yadda ya ce:

“Kusan makwanni 2 kenan da suka gabata, muka fara tantace ma’aikata a asibitocin mu kuma babban dalilin mu na tantancewar shine mu gano wadanda basu sabanta lasisin su ba, kawai sai muka ga nata lasisin ba irin namu bane.

“An yi saurin janyo hankalin mu, a matsayi na na shugaban kungiyar, aka mika min lasisin don in duba shi kuma na tabbatar da cewa na bogi ne.

“Na same ta don na yi mata wasu tambayoyi kuma na amshi sauran takardun ta. Mun gayyaci ‘yan sanda dama wadanda suka kama ta suka nufi ofishin su. Ba su musa ko zargi daya da aka yi mata ba; ta tabbatar da cewa duk takardun makarantar ta na bogi ne kuma akwai wanda ya hada mata su a Ibadan.”

Manema labarai daga Punch Metro sun tabbatar da yadda lamarin ya faru a ofishin ‘yan sanda na Lions Building.

Shugaban ma’aikatan jinya na jihar bai furta komai ba akan lamarin

Shugaban ma’aikatan jinya na hukumar lafiya ta jihar Legas, Olaide Animashaun ya tabbatar da kama matar amma bai furta komai ba dangane da lamarin.

Sakataren lafiya na jihar Legas, Ademuyiwa Eniayewun, ya ce ba zai iya cewa komai ba dangane da lamarin ta waya, inda ya ce sai dai wakilin The Punch ya je har ofishin sa don tattaunawa.

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, ya ce zai yi bincike akan kama matar da aka yi kuma zai tuntubi Punch. Har yanzu ba a ji komai ba daga wurin sa.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE