Karshen Duniya: Matashi ya yi kokarin kwakwale idanun mahaifiyarsa da ranta saboda wata bukatarsa, duba yadda lamarin ya faru


Yansanda sun kama wani matashi dan Yahoo mai suna Emma Ereegarnoma bayan ya yi kokarin kwakwale idanun mahaifiyarsa domin ya sami kudin tsafi. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Ya aikata wanan danyen aiki ne ranar Talata 14 ga watan Satumba a garin Okuokoko da ke karamar hukumar  Okpe a jihar Delta saboda Yana son ya sayi mota kirar Mercedes Benz.

Shafin isyaku.com ya samo cewa matashin ya gayyaci mahaifiyarsa ne zuwa gidansa cewa zai bata kyautar mamaki. Sai dai bayan ta isa gidan damta, sai ta tarar ya sa sautin na'urar kida kuma ya daga muryar na'urar da take waka sosai.

Bayan ta shiga gidan ne, kuma ya yi Mata maraba da zuwa, sai danta ya zagaya ta bayanta ya shake ta kuma ya yi kokarin kwakwale idanunta. Nan take mahaifiyarsa ta yi kokuwakokuwa ta kwace kanta kuma ta fita waje da gudu ta nemi agaji daga makwabta tana kururuwa.

Yanzu dai an kama danta Emma da ya yi barazanar cewa zai sayi mota kirar MercedesMercedes Benz GLK cikin wannan mako. Yansanda na ci gaba da bincike yayin da aka kai mahaifiyarsa wani Asibiti inda take samun kulawan Likita a garin Okuokoko. Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN