Yanzu yanzu: Zanga-zanga ta barke a jihar Bauchi, matasa sun tare hanyar Bauchi zuwa Dass


Wasu mazauna unguwar Birshin Fulani, da ke cikin garin Bauchi, sun tare hanyar Bauchi zuwa Dass suna zanga-zangar tabarbarewar tsaro a yankin.

BBC Hausa ta ruwaito cewa a halin yanzu masu ababen hawa na nan jibge a kan hanya sakamakon lamarin.

Kusan makonni biyu da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin inda suka kashe mutane biyu, ciki har da wani babban ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Bauchi, Malam Abubakar Muhammad.

An kuma yi garkuwa da wasu mutane a harin. Kwanaki kadan bayan faruwar lamarin ne aka kara sace wasu mutane.

Previous Post Next Post