Ta faru ta kare: Boko Haram sun fara koya wa 'yan bindiga yadda ake harbo jirgin sojoji


Yan Boko Haram sun fice daga sansanin su a Arewa maso Gabas don hada karfi da 'yan bindiga a Arewa maso Yamma, inda suke gudanar da horon makamai da garkuwa da mutane, kamar yadda majiyoyin soji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Juma'a.

Kungiyar Boko Haram na kara neman hadin kai da kungiyoyin ta'addanci tun bayan mutuwar shugabansu Abubakar Shekau a watannin da suka gabata, inji rahoton Punch.

Kungiyar ISWAP na shiga yankunan Boko Haram, inda take yakar masu biyayya ga Shekau, lamarin da ya kai har wasu ke 

mika wuya ga ISWAP din ko sojin Najeriya.

Sanarwar wata hukumar tsaro ta Najeriya a farkon wannan watan ta yi gargadin cewa wani kwamandan Boko Haram da sojojinsa na kasa na hijira daga sansanin su a jihar Borno zuwa jihar Kaduna a Arewa maso Yamma.

Manazarta sun ce akwai alamun da ke nuna cewa masu 'yan Boko Haram da 'yan bindigan suna habaka alaka mai zurfi inda duka biyun suka tsaya don samun hanyoyin samun makamai da aikata ta'addanci

Arewa maso Yammacin Najeriya ta dade tana fama da gungun 'yan bindiga, amma a bana, hare-hare da garkuwa da mutane sun karu.

Sojin Najeriya sun cafke kasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna Goma Sama'ila

Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar cafke shugaban ‘yan bindiga da barayin shanu, Alhaji Goma Sama’ila.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar SaharaReporters cewa, an damke Samaila ne a jihar Kaduna da yammacin Juma’a 24 ga watan Satumba.

Rahotannin shaidun gani da ido sun nuna cewa Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

An ce yana cikin wasu ayyunkan barna na garkuwa da mutane da dama a fadin jihohin.

Jihar Kaduna tana ci gaba da shan fama da barnar masu garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu daga 'yan bindiga.

Wata majiya ta ce: “Sojojin Najeriya sun cafke Goma Sama’ila, daya daga cikin “ wadanda ake nema” kuma kasurguman shugabannin 'yan bindiga da ke addabar Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da sojoji ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a yankin

Rahotun Jaridar Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN