Type Here to Get Search Results !

Abin da ya kamata ku sani kan cutar sikilar da ke shafar al'aurar maza

 

Cutar sikila ko amosanin jini na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Lalura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al'umma baki daya.

Bincike ya nuna cewa rabin masu sikilar da ake haifa duk shekara a Najeriya suke, kuma mafi yawa a arewacin kasar.

Likitoci sun ce wannan ciwo bai bar masu shi ta bangaren shafar lafiyar jima'insu ba. Ciwo ne da ke hana su rawar gaban hantsi sosai a wasu lokutan ta wannan fanni.

Ga maza, yawanci gabansu kan mike mike ya ki sauka, kwayoyin jini masu kamar lauje na makalewa a gabansu sai jinin ya ki fita ya taru a wajen, sai al'aurarsu ta mike ta ki sauka, wannan ciwo shi ake kira Priapism.

A wasu lokutan har sai an yi 'yar karamar tiyata, wasu kuma da an sanya kankara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban,'' in ji Dr Bashir Isa Waziri.

Cutar tashin alkalamin namiji ta 'priapism'

Tashin azzakari ba zai taba faruwa ba sai idan jini yana gudana a jikin dan adam yadda ya kamata.

A duk lokacin da sha'awar lafiyayyen namiji ta motsa, hanyoyin jinin da ke shiga mararsa da azzakarinsa za su kumbura.

Idan jinin ya taru a mara kuma jijiyoyin suka kulle suka hana jini zuwa ko ina hakan zai sa alkalamin nasa ya kara tsayi, da kumburi da kuma karfi.

Kuma da zarar sha'awar ta kwanta, jijiyoyin za su yi sanyi su kuma bude wa jini hanya ya fice daga inda ya taru a mara, wanda hakan zai sa alkalamin ya saki ya koma daidai.

Sai dai a lokacin kai da komon jini a marar namiji ya samu matsala, hakan na haifar da cutar tashin azzakari da a Turance ake kira 'priapism'.

'Priapism' cuta ce da ke sa azzakarin namiji ya kumbura ya tashi ya kuma yi karfi sosai na tsawon lokaci ba tare da ya kwanta ba. A wasu lokutan masu cutar sikila kan yi kwanaki cikin yanayin.

Ciwo na mai zafin gaske kamar yadda likitoci suka tabbatar, kuma yana faruwa ko da sha'awa ko babu.

Kazalika cutar kan iya kama babba ko yaro, amma ta fi kama masu cutar amosanin jini ko kuma sikila, da kuma masu fama da kansar jini.

A cewar Dakta Ibrahim Musa na asibitin koyarwa na Aminu Kano a birnin Kano da ke Najeriya, cutar karfin alkalamin namiji ta 'priapism' kan faru ne a lokacin da magudanun jini suka toshe marar namiji yayin da azzakarinsa ya tashi, kuma ya kan kasance a mike daga awa daya har zuwa kwana bakwai bai kwanta ba.

Bincike ya nuna cewa masu masu cutar sikila sun fi hadarin kamuwa da cutar, kasancewar suna da karancin sinadarin nitrate oxide da ke taimakawa wurin saukar azzakari, a cewar Dr Musa, wanda ya samu tallafi daga kungiyar likitocin jini ta Amurka, don gudanar da binciken gano maganin cutar.

Likitan ya kara da cewa baya ga tashin mazakutar, ta kan kuma yi ciwo tamkar na mai karkare.

A binciken da Dakta Ibrahim da abokan aikinsa suka gudanar, sun gano cewa cutar na yaduwa sosai a tsakanin jama'a musamman a kasashe irin Najeriya, amma kuma masu dauke da ita na jin kunyar fitowa su bayyana halin da suke ciki.

Duk da haka likitocin sun gudanar da wani bincike da suka samu bayanai daga mutum 500, kuma sun sami kashi 35 daga cikin su dauke da wannan cuta don jin yadda take zo musu.

Sun fahimci cewa priapism kan kama maza daga shekaru 12 zuwa sama akasarinsu masu cutar sikila.

Sai dai hakan ba yana nufin wanda ba shi da cutar sikila ba zai kamu ba, kamar yadda gwaji ya nuna a kan masu dauke da cutar da kuma ba su dauke da cutar sikila ko kansar jini.

Za a iya sa allura a zuke jinin da ya daskare a gaban namji wanda hakan yana sa a samu sauƙi

Magani

Kamar yadda Dakta Ibrahim Musa ya shaida, kawo yanzu babu takamaiman maganin cutar karfin alƙalamin namiji ta priapism.

A cewarsa cuta ce da mafi yawan wadanda take kamawa masu dauke da cutar sikila ne.

Sannan kashi 75 na masu fama da cutar sikila a nahiyar Afrika suke inda bincike ya yi karanci.

To amma a halin da ake ciki likitan ya ce sun fara bincike don samar da maganin wannan cuta.

Sai dai kuma idan cutar ta yi tsanani akwai taimakon gaggawa da likitocin ke bayarwa.

"Za a iya sa allura a zuke jinin da ya daskare a gaban namji wanda hakan yana sa a samu sauƙi."

"Akwai kuma tiyata inda za a buɗe wurin a yi ƙofa da jinin zai riƙa fita," in ji Dakta Ibrahim.

To amma a cewar likitan waɗannan hanyoyi kan iya haifar da matsalar mutuwar azzakari kwata-kwata idan ba a yi sa'a ba.

A kan haka likitan ke ganin abu mafi a'ala shi ne "samun magani da zai warkar da cutar a maimakon tiyata da ka iya haifar da wata matsala a gaba," a cewar likitan.

Karin wasu labaran da za ku so

Wani abu kuma shi ne a kan bai wa masu fama da cutar priapism wasu magunguna da ke taimaka musu jin sauƙi ko warkar da su, amma kuma suma suna dauke da tasu matsalar.

"Kamar yanzu akwai maganin da muke ba su amma wani lokaci zai iya sa nonon namiji ya kumbura kamar na mace.

"Ka ga ko da yana magani matsalarsa ta sa ba a son amfani da shi saboda ba wanda zai so yana namiji ya yi nono kamar mace," in ji Dakta Ibrahim.

Sai dai wani abu mai daɗin ji shi ne a ta bakin likitan sun yi nisa wurin samar da ainihin maganin cutar musamman ga masu cutukan sikila.

Dan Najeriya da ke binciken gano maganin cutar sikila

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Burtaniya wato NHS ta gano, akwai abubuwan da mai fama da wannan cuta zai riƙa yi don rage raɗadinta da suka haɗa da:

Haka kuma a cewar NHS mai wannan cuta kada ya kuskura ya saka wa azzakarin nasa ƙankara ko ruwan sanyi.

Haka kuma dole ne ya haƙura da jima'i ko kuma wasa da gabansa har maniyyi ya fito masa.

Sannan kuma a cewar NHS mai cutar priapism ba zai sha giya ko sigari ba a sanda cutar ta tasar masa.

Wasu likitoci sun gano cewa akwai hanyoyin riga-kafi daga cutar da suka hada da motsa jiki akai-akai, saboda daskarewar jini kan iya haifar da ita ga masu sikila da masu cutar kansar jini dama wadanda ba su da ko daya daga wadannan cututtuka.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies