Shirin N-Power: Gwamnati Ta Fara Biyan Bashi Ga Mutum 14,021


Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana cewa a yanzu ta fara yin biyan ƙarshe na bashin da ya rage ga masu cin moriyar shirin tallafi na N-Power kashi na ‘A’ da ‘B’ su 14,021.

Hakan ya biyo bayan kammala warware ‘yar mishkilar da aka samu a tsarin da ake amfani da shi wajen tattara bayanan biyan kuɗin.

Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura Alƙali, shi ne ya bayyana haka a cikin wata takarda ga manema labarai da ya saki a Abuja a madadin ministar ma’aikatar, wato Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Alƙali ya ce tun a cikin watan Maris 2020 ne asusun ajiya na masu cin moriyar shirin su 14,021 su ka samu matsala, inda tsarin biyan kuɗin na Gwamnatin Tarayya mai suna ‘Integrated Financial Management Information System’ (GIFMIS) ya dakatar da biyan nasu kuɗin saboda wasu dalilai daban-daban waɗanda su ka haɗa da:

1) mallakar asusun banki sama da ɗaya na masu cin moriyar shirin, da kuma

2) karɓar wasu kuɗin daban a asusun banki na masu cin moriyar shirin kamar su albashi da alawus-alawus daga ma’aikatu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya daban-daban, na aikin dindindin ko na wasu shirye-shiryen da su ka shiga.

Ya ce waɗannan hidindimun sun saɓa wa ƙa’idojin shirin sa-kai na N-Power wanda ka iya jawo babban laifi da ma cin hanci da rashawa.

Babban Sakataren ya ƙara da cewa ma’aikatar ta yi wani bincike mai zurfi tare da haɗin gwiwar ma’aikatun gwamnati da su ka dace kuma zuwa yanzu an warware mishkilar da ta shafi asusun mutum 9,066 ‘yan sa-kai a shirin, kuma har an fara biyan su.

Ya ce, “Bisa ga wannan tantancewar, yanzu an soma biyan alawus ɗin watanni biyar da waɗannan ‘yan sa kan ke bi, kowanne wata a kan jimillar N150,000.00. Alawus ɗin sauran mutum 4,955 kuwa an riƙe su har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi.

“Idan an tabbatar mutum ya karya ƙa’idojin yarjejeniyar da aka yi, to za a yi wa irin waɗannan masu karya ƙa’idar hukuncin da ya kamata kamar yadda doka ta tanada.”

Haka kuma Alƙali ya ce akasin surutun da ake yaɗawa a cikin jama’a, wannan tsari babbar manuniya ce ta irim ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi na ganin ta magance wannan matsala maras daɗi da aka samu ta hanya fisabilillahi domin tsare gaskiya tare da kauce wa sake aukuwar hakan a nan gaba.

Ya ce, “Kamar dai yadda ake ta faɗa, binciken da ma’aikatar ta yi shi ne ya fi dacewa da ƙasar nan kuma babbar manufar sa ita ce a kafa ingantaccen Shirin Inganta Rayuwa na Ƙasa, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) tare da tabbatar da cewa ana gudanar da shi cikin aminci kamar yadda mai girma Shugaban Ƙasa ya ƙudiri aniyar tabbatar da tsare gaskiya da amana a wajen aiwatar da shirin a kowane lokaci.”

Alƙali ya ce ma’aikatar ba ta ji daɗin tsaikon da aka samu ba wajen kammala wannan tsarin, “to amma ta na tabbatar wa da jama’a cewa ba za ta iya yin watsi da tsare gaskiya da amana ba a dukkan ayyukan ta.”

Rahotun leadership Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN