Type Here to Get Search Results !

Yadda binciken BBC ya gano ba a fara aikin wutar Mambila ba shekara 40 da fara maganar aikin


Wani bincike da BBC Hausa ta gudanar ya bankado cewa ba a yi komai ba a wurin da aka ware domin aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya shekara arba'in da fara maganar aikin.

Tun a shekarar 1982 ne lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari aka fara maganar tashar wutar wacce a lokacin aka tsara za ta samar da wuta megawat 2,600.

Gwamnatoci da suka shude sun sake fasalta aikin wutar inda a shekarar 2012 karkashin shugaba Goodluck Jonathan aka kara yawan megawat da tashar za ta samar zuwa 3050.

Takaitaccen tarihin wutar mambila

A shekarar 1982 ne aka bijiro da maganar aikin wutar lantarkin ta Mambila.

Daga lokacin gwamnatoci dabdan-daban sunyi ta sauya tsarin aikin wutar.

Misali tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yayin kaddamar da fara aikin tashar wutar a ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2007 a garin Gembu da ke kan tsaunin Mambila, ya bayyana cewa tashar za ta samar da megawat 2600 na wuta kuma ya sa an gina ofisoshi da gidaje inda ma'aikata da za su yi aikin za su zauna tare da ajiye kayan aiki.

Bayan Shugaba Obasanjo ya sauka daga kan karagar mulki, an sake fadada fasalin aikin a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a shekarar 2012 inda aka kara shi zuwa megawat 3050.

Sai dai kuma a watan Yulin shekarar 2021 gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rage yawan megawatt din zuwa 1,520.

Tsohon ministan wuta Injiya Saleh Mamman ya ce an dauki matakin ne domin ganin ya gudana.

Abunda BBC ta gano

Binciken da BBC ta gudanar yayin ziyarar da wakilinta Salihu Adamu Usman ya kai makwararar ruwa na 'Tambi Waterfalls' a tsaunin Mambila wanda shi ne jigo daga cikin wurare 3 da za a kafa cibiyar wutar lantarkin Mambila domin ganin yadda wurin yake ya gano cewa ba a fara aikin ba.

Babu hanyar mota da za ta kai mutum zuwa kan tsaunin da za a yi aikin kuma babura ne kadai ke iya zuwa sai kuma kafa.

Ana shafe sa'o'i 5 ana tafiya kan babur sai kuma sa'a daya ta tafiyar kafa.

Bayan isa filin da za a yi aikin wutar, BBC ta tarar babu aikin da aka yi a wurin.

A tsawon wadannan shekarun dai an yi ta maganganu daban-daban kan inda aka kwana wajen aiwatar da aikin da ake sa ran zai samar wa Najeriya isasshiyar wutar lantarki.

Ko da a shekarar 2020 ma a wata hira da BBC, tsohon ministan wutar lantarki Injiya Saleh Mamman ya ce akwai tatsuniya kan batun wutar ta Mambila.

Idan har aikin ya kammala tashar za ta kasance mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a nahiyar Afirka.

Najeriya na samar da megawat na wuta tsakanin 5,000 zuwa 5400 a lokaci da dukkan tashoshin samar da wuta na kasar ke cikakken aiki.

Ana yada hotunanbogi kan aikin wutar Mambila

Bayanan hoto, Nan ne ainihin makwararar ruwa ta Tambi inda aka shirya kafa tashar wutar lantarkin

BBC ta gano cewa idan mutum ya leka intanet zai ga wasu hotuna da dama na bogi da ake ta yadawa da sunan tashar wutar Mambila to amma wannan hoto na sama shi ne ainihin wuri da aka kebe domin aikin.

Akasarin hotunan da ake wallafawa a intanet hotuna ne na madatsar ruwa ta Kashimbila wacce ke karamar hukumar Takum da ke kudancin jihar Taraba.

Ita kuwa tashar wutar Mambila a yankin Taraba ta tsakiya za'a kafata.

An kirkiro dam din Kashimbila ne domin rage karfin ruwa da ke kwararowa daga kan tsaunuka da ke yankin don rage ambaliya da kuma inganta harkar noman rani da kamun kifi.

Dam din Kashimbila na karkashin kulawar ma'aikatar albarkatun ruwa ce ta Najeriya, shi kuwa aikin wutar Mambila aiki ne da ke karkashin ma'aikatar wuta ta kasar.

BBC ta yi kokarin jin martanin ma'aikatar wutar lantarki ta Najeriya kan aikin wutar ta Mambila amma hakar ta ba ta cimma ruwa ba.

Za mu kawo muku martanin ma'aikatar da zarar ya samu.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies