An kama gurgu mai shekara 22 bisa zargin garkuwa da mutane


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi ram da wani matashin gurgu mai shekaru 22 mai suna Buhari Haruna daga karamar hukumar Kankia ta jihar.

Ana zargin gurgu Buhari Haruna da barazanar sace wani idan ba a biya shi kudi har naira miliyan biyu ba, LIB suka ruwaito

.A yayin damke wanda ake zargin tare da nunawa manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce an kama Haruna ne yayin da ya je karbar kudin fansan kuma yayi basaja kamar sunkin biredi a wurin da aka yi za a karba.

Isah ya ce, kamen Haruna ya bayyana cewa, hatta wadanda ba a tsammanin za su yi laifi a yanzu suna amfani da mummunar damar wurin satar jama'a.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan kamensa, Haruna bai musanta laifin da ake zarginsa ba.

Ya ce ya kira mutumin da ke makwabcinsa ne tare da yi masa barazanar cewa in har bai biya kudi naira miliyan biyu ba, zai yi garkuwa da shi.

Ya ce ya yi nadamar abinda ya yi, duk da shi mai nakasa ne, ya na rokon yafiya kuma 'yan sandan su yi masa rangwame, LIB ta ruwaito.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN