Matsayin jihar Kebbi zai ba ka kunya a Jerin jihohi 10 da sukafi kowa samun kudin shiga da kuma 5 na kasan-kasa


A ranar Juma'a, 16 ga watan Afrilu, hukumar lissafe-lissafen Najeriya (NBS) ta saki adadin kudin shiga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya suka samu a rubu'in karshe na shekarar 2020 da kuma na shekarar gaba daya.

Rahoton ya nuna cewa jihohin Najeriya gaba daya da FCT Abuja sun samu jimillan kudin shiga N1.31 trillion a 2020.

Legit ta lura cewa kudin da aka samu a 2020 yayi da kasa da abinda aka samu 2019 da N1.33 trillion.

Hakan na nuna cewa an samu nuksanin -1.93% (2019/2020)

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa wannan ya faru ne sakamakon bullar cutar Korona a 2020.

A cewar rahoton, jihar Legas ce ta sama wajen samun kudin shiga N418.99 billion, sannan kuma jihar Ribas da ta samu N117.19 billion.

Ga jerin jihohi 10 dake sama wajen kudin shiga:

1. Lagos - N418.99 billion

2. Rivers - N117.19 billion

3. FCT - N92.05 billion

4. Delta - N59.73 billion

5. Kaduna - N50.76 billion

6. Ogun - N50.74 billion

7. Oyo - N38.04 billion

8. Kano - N31.81 billion

9. Akwa Ibom - N30.69 billion

10. Anambra - N28.00 billion

Jerin jihohi biyar na kasa

1. Jigawa - N8.66 billion

2. Gombe - N8.53 billion

3. Adamawa - N8.32 billion

4. Taraba - N8.11 billion

5. Yobe - N7.77 billion

Jihohin da dama ba za su iya sauke nauyin da ke kansu ba domin gwamnatin tarayya za ta rasa kaso na abin da take samu daga haraji daga wajen gwamnatin tarayya ba.

Mafi yawan jihohi sun dogara ne da kason da suke samu daga asusun hadaka na FAAC saboda gwamnoninsu ba su samun kudin-shiga.

Jihohin Ribas da Legas ne suke tattara 70% na harajin kayan masarufi a Najeriya, amma a karshe ana raba kudin ne tare da sauran gwamnonin jihohi 36

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ya shigar da kara a kotu ya dage a kan bakararsa, yace ko sama da kasa za su hade ba zai bar FIRS ta karbi harajinsu ba.

Binciken da jaridar DailyTrust ta wallafa ya nuna cewa a halin yanzu jihohi 30 ba za su iya rike kansu ba idan abin da gwamnati take samu daga harajin VAT ya yi kasa.

Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatad da gwamnatocin jihar Rivers da Legas daga karbar kudin harajin VAT da hukumar FIRS ta saba karba daga hannun kamfanoni.

A hukuncin da Alkali Haruna Simon Tsanami ya yanke ranar Juma'a, ya bada umurnin cewa ayi watsi da sabuwar dokar da majalisar wakilan jihar Rivers ta kafa kuma gwamnan Wike ya rattafa hannu, rahoton DailyTrust.

Hakazalika majalisar dokokin Legas ta samar da irin wannan doka kuma gwamnan nan Babajide Sanwoolu ya rattafa hannu.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN