Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi


Sanannen malamin addinin Islama mazaunin Kaduna, ya kara tabbatar wa da jama'a cewa a koda yasuhe ya na samun damar tattaunawa da 'yan fashin dajin da suka addabi arewacin Najeriya.

A takardar da malamin ya fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun 'yan bindiga sun sanar da shi cewa luguden ruwan wutan da sojin saman ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da 'ya'yansu, domin kuwa suna da salon kauce musu, Punch ta ruwaito.

Gumi ya ce 'yan bindigan sun kware tare da zama 'yan hannu wurin kauce wa duk wani bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa da kyar a iya kama su ko halaka su.

A wata takarda da TheCable ta gani, ya bayyana cewa:

"Abinda ba dole ku sani ba shi ne, 'yan bindigan sun kirkiro hanyoyin tsere wa luguden wuta ta sama. Sun sanar da mu cewa, za ku iya kashe matansu da 'ya'yansu ne kawai ta wannan harin.

"Abin nufi shi ne, idan aka matsanta musu a Zamfara, babu shakka za su sauya wuraren zama. Toh dukkan Najeriya ce za ta kasance a wannan halin?

Wurin karin bayani, fitaccen malamin ya bayyana cewa bayanai masu kyau, tsarin jami'ai nagari da kuma hada kai da makiyaya, sasanci duk suna cikin hanyoyin shawo kan matsalar 'yan fashin daji.

Gumi ya kara da cewa:

"A zancen gaskiya, shari'a ce ke kare hakkokin jama'a. Kudi da lokaci da aka yi amfani da su da kyau babu shakka za su kashe cutar kuma zai gyara kasar nan, ya cire mata cutar ta'addanci da gurbatattun shugabanni."

Legit News

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari