Karshen Duniya ya zo: Yadda wa da kaninsa suka yi wa mahaifiyarsu cikin shege har sau uku kuma ta haifi yara uku


Rundunar tsaron farin kaya na NSCDC a jihar Kwara ta kama wani mutum dan asalin kasar jamhuriyar Benin , mai suna Adamu Sabi Sime, bisa zargin yi wa mahaifiyarsa cikin shege har sau uku. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Kakakin rundunar na jihar Kwara Babawale Afolabi, ya sanar wa manema labarai a birnin Ilorin ranar Asabar 11 ga watan Satumba. Ya ce mahaifiyar Adamu ta haifi yara uku da ya yi mata ciki shi da kanshi.

Ya ce Hakimin kauyen Mosne a karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, mai suna Mallam Bandede ne ya kai karar Fati, mahaifiyar da danta Adamu bisa zargin abin da suke aikatawa a kauyen. Sakamakon haka jami'an sashen binciken sirri na rundunar suka shiga bincike da ya tabbatar da cewa Adamu ya yi wa mahaifiyarsa Fati ciki har sau uku kuma ta haifi yara uku sakamakon  ciki da ya yi mata.

Kazalika jami'an sun gano cewa hatta kanin Adamu yana jima'i da mahaifiyarsa. Sai dai ya tsere lokacin da jami'an suka je bincike.

Rundunar NSCDC ta jihar Kwara ta mika wadanda ake zargin ga hukumar shige da fice na jihar Kwara bayan ta gano cewa yan kasar Benin ne kuma basu da takardun izinin zama a Najeriya.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN