Type Here to Get Search Results !

Karya ne babu wanda ya taba kera cajar wayar salula a jihar Kebbi - Kwararren masani


Wani masanin harkar ingizon wayar salula da silar tsaro na yanar gizo Isyaku Garba Zuru, ya karyata zancen cewa wasu yara sun kera cajar wayar salula a garin Birnin kebbi.

Isyaku ya yi wadannan kalaman ne yayin wata tattaunawa da wasu masana abokan aiki da suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Taushi Plaza kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.

Ya ce " Akwai wasu Yan siyasa da suka alakanta kansu da wasu mutane da ke harkar wayar salula a garin Birnin kebbi. Wadannan mutane sun ce wai yaran sun kera cajar wayar salula, har da nuna wani kwarya-kwaryar caja cewa yaran ne suka kera"

Ya Kara da cewa " Wannan zancen karya be. Na shekara 10 cikin harkar daidaita ingizon wayar salula, kuma kasancewa mutum na farko dan asalin jihar Kebbi da ya fara wannan aiki a tarihin jihar Kebbi.

Wannan ya bani damar gane iya karfin fikirar kowane yaro idan dai dangane da gyaran wayar salula ne ko ingizonsa a cikin garin Birnin kebbi sakamakon huldar mu kan sanaar yau da gobe kuma kasancewar mu manya a ciki a wancan lokaci.

Kuma zan tabbatar maku da cewa a yanzu dai kam, bamu kai matakin kera caja ba a jihar Kebbi saboda dalilai da suka hada da rashin wadataccen ilimin fasahar aikatau wajen kirkirar tsarin gina na'ura ko abin da ke da alaka da haka.

Idan har wani ya kera caja a garin Birnin kebbi, wane kwararren masani ne, kampani ko ma'aikata ta tabbatar da jngancin wanna caja. Akwai abin da ake kira "quality assurance" a turance, wa ya tabbatar da gaskiya balle ingancin kera wannan caja? Da miye aka hada suka bayar da silar tsarin ginau wajen sarrafa fasahar yin wannn caja? A Ina aka yi wannan caja a cikin grin Birnin kebbi kuma wa ye ya kera cajar? Za mu sami tabbacin cewa ba wai an yi kofin wata kerarrar caja bane aka zo aka ce an kera caja?"

Kwararrun masanan sun jinjina wa Isyaku Garba, Mr Joshua ya ce " Ina samun Labaran shafinka a kasar Kamaru da na je wajen wani biki, a can Douala na karanta Labaran shafinka. Ina da abokai a Jihohin California, Texas, Houston, New York da Illinois duk suna karanta labaranka a kasar Amurka"


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies