Ko da gaske ne jam'iyar APC za ta ba Goodluck Jonathan tikitin takarar shugaban kasa a 2023?

 

Jam’iyyar APC ta ce ba ta tabbatar wa da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tabbacin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakataren CECPC, John Akpanudoedehe ya bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce komawar mutum jam’iyya ba ya bayar da tabbacin a bashi wani matsayin a jam’iyya.

Akpanudoedehe ya yi karin haske ne a kan sauya fahimtar sa da aka yi na rangwamen da NEC ta bai wa sababbin mambobin jam’iyya da masu sauya sheka a wani taron su da suka yi a ranar 8 ga watan Disamban 2020.

Yayin wani shirin gidan talabijin, ya ce duk wani dan jam’iyya komai matsayin sa sai ya bi dokar zabe wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Ya tsaya akan batun rangwamen NEC ba zai tsaya a kan kowa ba, Daily Nigerian ta wallafa.

Kamar yadda sakataren ya ce:

“Rangwamen zai shafi kowa da kowa ba kamar yadda mutane suke canja maganar ba.

“Ba za a fifita mutum a bashi wani matsayi na daban ba har da damar tsayawa takara kawai saboda sabon dan jam’iyya ne. Duk mai neman takara dole ne ya bi duk tsarin da kundin tsarin mulkin APC ya tanadar.”

Akpanudoedehe ya tunatar da yadda NEC din jam’iyya ta shirya bayar da rangwame ga sababbin ‘yan jam’iyya da masu burin shiga jam’iyyar don ya tsaya takarar wani matsayi a jam’iyyar APC kasancewar ita ce jam’iyyar da ake yayi a halin yanzu.

Ya bayyana cewa batun da NEC tayi na , “APC za ta samar wa sababbin ‘yan Jam’iyya matsayi na musamman sai dai ba tikitin tsayawa takara ba.”

A cewar sa:

“A wata tattaunawa da aka yi da ni a gidan talabijin a kan maganar da tayi ta yaduwa a kan Goodluck Jonathan zai koma jam’iyyar APC, magana ta ita ce NEC ta tabbatar da bai wa sababbin ‘yan jam’iyya rangwame na daban.

“Sai dai rangwamen ba a kebantar da shi ga wasu mutane na daban ba kamar yadda mutane su ka yi ta yadawa. Duk mai neman matsayi zai dage ya bi dokokin da kundin tsarin APC ya tanadar.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN