Yanzu yanzu: Mutum biyu sun mutu bayan ginin Chochi ya rufta wa masu ibada (Hotuna)


Mutum biyu sun mutu bayan ginin Mujami'ar da suke bauta a ciki ya rufta kansu a jihar Taraba ranar Lahadi 11 ga watan Satumba. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne a Mujami'ar Holy Ghost Church da ke garin Abeda Pave a Mazabar  Chachanji da ke karamar hukumar Takun a jihar Taraba .

Mun samo cewa akwai mutane da ba a fayyace adadinsu ba da suka sami raunuka daban daban sakamakon ruftawar ginin yayin da jama'a ke tsakar yin ibada a Mujami'ar.

Rahotanni sun ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama da aka yi ta yi a garin.
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari