A fara gwada ƙwaƙwalen ƴan siyasa kafin a gwada na malamai


Majalisar malamai a Kano ta ƙalubalanci matakin gwamnatin jihar na samar da wata doka ta hana malaman jihar wa'azi har sai sun kawo takardar shaida daga asibiti da ke nuna cewa ba su da matsalar ƙwakwalwa.

Majalisar malaman ta Kano ta shaida wa BBC cewar 'yan siyasa masu riƙe da muƙamai ya kamata a fara saka wa wannan doka, kafin a ce an waiwayi kan su malamai.

A cewar shugaban majalisar malaman ta Kano Malam Ibrahim Khalil, bai kamata a yi musu kuɗin goro ba don mutum ɗaya daga cikinsu ya yi kuskure.

"Gwamna ne, sarki ne, duk wani wanda yake da wani muƙami, masu tura sojojin baka da sojojin baka su ya kamata a fara yi wa wannan don su suka fi kowa jan mutane ga hanyar da ba su dace ba," in ji Sheikh Ibrahim.

Ya kuma ce babu wanda ya isa ya hana malamai yin wa'azi tun da aiki ne na annabawa kuma aikin Allah ne inda ya ce bai ka mata a saka malamai a wannan rukunin ba domin sun fi kowa hankali, a cewarsa.

Wannan dokar dai da gwamnatin Kano take so ta yi, ba ta rasa nasaba da batun gwajin ƙwaƙwalwa da kotun jihar ta sa a yi wa ɗaya daga cikin malaman jihar wato Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bayan gaza amsa tambayoyin da alkalin kotu ya yi masa ranar 2 ga watan Satumba.

Malam Ibrahim Ƙhalil ya kuma ce duk wani wanda aka kama da laifi ko kuma kuskure a Kano ko waye shi ya kamata a duba ƙwaƙwalwarsa.

Malam Ibahim ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin a fara tunanin ɗaukar wannan mataki amma ya ce idan aka tuntuɓe su za su bayar da bayani.

Sai dai a nasa ɓangaren, kwamishinan harkokin addini na Kano, Dakta Muhammad Taha Adam wanda aka fi sani da Baba Imposible, ya ce wannan doka da ma'aikatarsa ke son gabatarwa gaban majalisar dokoki ta jihar Kano, daidai take da dokar da gwamnatin jihar ta yi ta duk wanda za a bai wa duk wani muƙami sai an yi masa gwaji na miyagun ƙwayoyi.

A cewarsa, daga ma'aikatarsa ta kula da harkokin addini za su aika da kudiri zuwa majalisar zartarwa ta jihar sai kuma majalisar dokoki .

"Duk malamin da zai gabatar da wani wa'azi, sai ya kawo satifiket na ƙwaƙwalwarsa lafiya kuma ba ya shaye-shaye.

"Cututtukan da malamai suke harbawa cikin al'umma sun fi cutar AIDS cutarwa," in ji Baba Impossible.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN