Mutanen gari sun ƙona wasu ƴan bindiga da aka kama a Tangaza


A garin Tangaza da ke jihar Sokoto, bayan da wasu barayin daji suka kashe wasu mutan garin biyu, mutanen garin sun bi sawusnu kuma sun yi nasarar kama shidda daga ciki.

Jama’ar garin dai sun harziƙa inda suka kashe su tare da kona gawarwakinsu.

A jihar Zamfara kuwa, jama’ar yankin garin Gurbin Baure sun ce yankinsu bai ma san ko jami'an tsaro na farautar ɓarayin ba saboda babu wani sauyi da suka samu dangane da ɓarayin dajin da suka addabe su.

Abdou Halilou ya yi duba kan wannan lamari. Saurari rahotonsa:

BBC

Video caption: Rahoton Abdou Ha
Previous Post Next Post