Da duminsa: A karamar hukumar Shanga jihar Kebbi yan bindiga sun kashe mutane da dama yan gida daya, sun harbi wasu mutum 5 da bindiga


Yan bindigan daji sun halaka mutum biyar yan gida daya suka kuma harbi wasu mutum biyar da bindiga a kauyen Uchukku da ke karamar hukumar Shanga a kudancin jihar Kebbi.

Yushau Garba Shanga ya ce Yan bindigan sun farmaki kauyen Uchukku ne da misalin karfe 1:50 na dare suka bukaci kauyawa su mika masu shanayensu ko kuma su kashe su.

Daya daga cikin wadanda farmakin ya rutsa da shi amma yake jinyar raunukan harsashi a asibiti ya ce:

"Bayan Yan bindigan sun harbe yayanmu, sun harbe baban mu kuma suka harbe sauran kannan mu. Mu kuma suka yi mana rauni, har da 'yar karamar yarinya da batasan komi ba, suka harbeta a kafa. A cikin wadanda suka harba mutum hudu, nan take suka mutu a wajen. Dayan kuma rai ya yi halinsa ne lokacin da suka zo asibiti".

Rahotanni sun ce al'ummar wannan yanki, wanda akasari yan kabilar Dukkawa ne, suna tattakin yin hijira zuwa garin Shanga don neman mafaka.

Kafofin labarai da dama sun sha labarta cewa Yan bindigan daji da ke fuskantar saukar aradun hare haren sojin Najeriya ba kakkautawa a Zamfara, sun kazama wasu jihohi masu makwabta da jihar Zamfara domin guje wa farmakin sojin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN