Yansanda sun kama wani soja, abin da ya aikata zai ba ka mamaki


Yan sanda a jihar Nasarawa sun cafke wani sojan bogi, Timothy Emmanuel wanda ke yawo cikin kayan sojoji.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa matashin mai shekaru 28 ya kasance yana yiwa wani jami'in sojan Najeriya sojan gona, a cewar kwamishinan 'yan sandan jihar, Adesina Soyemi.

Soyemi ya ce an gurfanar da Emmanuel, wanda dan asalin jihar Filato ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, tare da wasu mutane 60 da ake zargi da aikata laifuka daban -daban.

An samu bindiga kirar AK-49, mujalla biyu da motar Toyota Corolla yayin da mai laifin mai shekaru 28 ke tafiya akan hanyar B.A.D a karamar hukumar Lafiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Soyemi ya bayyana cewa wanda ake zargin yana aikata miyagun ayyuka a Karu da Lafiya kafin a kama shi.

A cewarsa, ana binciken Emmanuel a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Lafiya.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN