Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Jam'iyar PDP a jihar Kebbi ta kori Kabiru Tanimu, Bello S. Yaki, Maria Waziri, Haruna D. Saidu daga jam'iyar


Jam'iyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kebbi ta kori tsohon Ministan ayyukan musamman kuma babban Lauya Kabiru Tanimu (SAN) tare da wasu mutane uku daga jam'iyar bisa zargin aikata ba daidai ba. Shafin isyaku.com ya samo.

Daily Trust ta ruwaito cewa Mataimakin shugaban jam'iyar na shiyar Kebbi ta tsakiya Garba Abubakar Besse ya sanar wa Wakilin Daily Trust yayin tattaunawa ta wayar salula ranar Lahadi.

Ya ce sauran wadanda jam'iyar ta kora a jihar Kebbi, sun hada da shugabar mata na jam'iyar na kasa Hajiya Maria Umaru Waziri, da shugaban jam'iyar na jihar Kebbi Haruna D. Sa’idu, da kuma Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam'iyar PDP a zaben 2015 Janar Sarkin Yaki Bello.

Ya ce an kore su daga jam'iyar ne bayan sun mayar da Sakatariyar jam'iyar zuwa Abuja kuma suka yi wuf da takardun cikewa na neman tantance yan jamiyar kafin taron jam'iyar da ake son a yi saboda biyan bukatar kansu da na abokansu.

Bello S. Yaki bai ce uffan ba da aka tuntube shi a wayar salula , ya ce yana cikin wani taron tattaunawa. Kazalika sauran wadanda aka kora basu amsa kiraye-kirayen wayar salula ko sakon Text da aka aika masu ba kan lamarin. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies