Jarirai na kamuwa da cutukan da uwa ta dauka wajen jima'i


Wasu hanyoyi uku da mata masu juna biyu ke iya yada wasu cututtuka zuwa ga jariransu su ne, a ciki da lokacin haihuwa da kuma yayin shayarwa, in ji likitoci.

Wadannan cututtuka suna da dama, amma wasu daga cikinsu su ne, ciwon hanta, cutar sanyi, cutar Tetanus, cutar karambau da kuma cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya.

Kungiyar kwararrun likitocin mata ta Amurka, ACOG, ta bayyana cutar HIV da cewa tana daya daga cikin cututtukan da uwa ke yadawa zuwa ga danta.

Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake daukar kwayar cutar HIV dai shi ne ta hanyar jini.

Haka kuma da zarar kwayar cutar ta shiga jini sai ta mamaye kwayoyin halittar da ake kira CD4, a likitance.

Wadannan kwayoyin halittun su ne jiga-jigan garkuwar jikin dan adam.

Saboda haka, sai garkuwar ta yi rauni kuma jiki ya kasa yaki da kwayoyin cututtukan da za su kama mutum.

ACOG ta ce akwai wasu hanyoyin wadanda idan mace mai ciki kuma mai HIV ta bisu,to akwai yiyuwar kashi 99 cikin dari ba za ta yada cutar ga jaririnta ba.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN